Mun damke yan luwadi 12, yan fyade 14, karuwai 200 a Jigawa - Hizbah

Mun damke yan luwadi 12, yan fyade 14, karuwai 200 a Jigawa - Hizbah

Hukumar kawar da batanci da rashin tarbiyya a fuskan adinin Musulunci ta jihar Jigawa wacce akafi sani da Hizbah ta bayyana yawan mufsidan da ta damke a jihar a shekarar 2019 da ya shude.

Hukumar ta ce akalla masu aikata luwadi 14, masu yiwa mata fyade 14 da karuwai 200 aka kama a shekara.

Yayinda yake jawabi a hedkwatan hukumar dake Dutse, babbar birnin jihar, kwamandan hukumar, Ibrahim Dahiri Garki ya ce an damke wadannan mutane ne tsakanin watan Junairu zuwa Disamban 2019.

Ya ce a cikin shekarar, an tsinci sabbin jarirai 14 da iyayensu suka jefar.

Yace an mika dukkan wadanda aka kama ga hukumar yan sanda domin hukuntasu bisa doka.

A baya mun kawo Hukumar Hizbah, shiyar jihar Jigawa a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta kashe auren dole 330 da aka gudanar a shekarar 2019 bayan amaren sun gudu daga gidajen.

Shugaban hukumar, Ibrahim Garki, ya bayyanawa Premium Times cewa sun kashe auren dolen ne bayan amaren suka kai kara ofishohin Hizbah dake jihar.

Ya ce bayan kashe auren, hukumar ta mayar da amaren wajen iyayensu.

Hakazalika hukumar ta baiwa iyayen shawara su sanya 'yan matan makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel