Saurayi ya yiwa 'yar bautar kasa fyade ya kuma dauki bidiyonta tsirara

Saurayi ya yiwa 'yar bautar kasa fyade ya kuma dauki bidiyonta tsirara

- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani mai gyaran takalma da laifin yi wa 'yar bautar kasa fyade

- Bayan yi mata fyaden, ya nadi bidiyonta tsirara wanda ya tura wa abokan shi

- Mai gyaran takalman wanda yayi ikirarin budurwar shi ce, yace yayi mata fyade ne don tayi yunkurin tsinke soyayyarsu

Hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mai gyaran takalma mai suna Olamide Babayemi a kan laifin fyade ga 'yar bautar kasa da kuma yunkurin kasheta.

An gano cewa, mai gyaran takalmin dan shekaru 25 ya yi wa 'yar bautar kasa mai shekaru 22 fyade ne a rukunin gidaje na Greenland dake yankin Mowe na jihar. Ya nadi bidiyonta tsirara bayan nan ya tura wa abokan shi.

Wacce aka yi wa fyaden tayi ikirarin cewa ta ba Babayemi N18,000 don ya siya mata waya amma har yanzu shiru.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin 'yan sandan jihar, tace anyi wa 'yar bautan kasar fyade ne bayan da taje karbar wayar a gidan saurayin.

Bayan tuhumar saurayin da aka yi, yace suna soyayya ne da budurwar kuma ya yi mata fyade ne bayan da ta dena son shi bayan ta kammala digirinta.

KU KARANTA: Mutumin da aka shekara 12 ana nema, an gano shi a kungurmin daji ya gina gida yana zaune abin shi

"Wanda ake zargin ya kira ta a ranar 2 ga watan Janairu a kan tazo ta karba wayarta. Tana isa yasa mata karfi inda ya cire mata kaya tare da yi mata fyade. Daga nan ne ya jika kayanta a ruwa kuma yayi amfani da wayar shi ya dau bidiyonta tsirara wanda ya tura wa abokan shi.

"A lokacin da ya gano zata kai wa 'yan sanda kara, sai yayi kokarin kasheta amma sai wayar mahaifiyar shi ta katse shi. A nan ne 'yar bautan kasar ta samu tseratar da rayuwarta ta gudu.

"Tuni DPO ya tura jami'ai don su kama wanda ake zargin amma sai ya gudu. A ranar 4 ga watan Janairu ne mahaifiyar shi ta kaishi gaban 'yan sandan." Cewar takardar.

Bayan tuhumar shi da aka yi, ya dora laifi a kan budurwar saboda ta yi yunkurin barin shi bayan kammala digirinta.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bukaci a mayar da wanda ake zargi zuwa sashi na musamman na manyan laifuka don cigaba da bincike tare da gurfanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel