Kin saka kaya bayan anyi wanka: Mai aiki ta shake 'yar shekaru 2 har lahira

Kin saka kaya bayan anyi wanka: Mai aiki ta shake 'yar shekaru 2 har lahira

Mummunan lamarin mai matukar tashin hankali ya auku ne a ranar Asabar, 11 ga watan Janairu 2020 a titin Ihechiowa dake kusa da titin MCC a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Mai aiki 'yar shekaru 16 a duniya ta hallaka 'yar masu gida mai shekaru biyu a duniya har lahira.

An gano cewa, mai aikin ta shake 'yar masu gidan ne har ta sheka lahira bayan da ta umarceta ta saka kaya taki. Mai aikin tayi wa yarinyar wanka ne amma yarinta ta hana karamar yarinyar saka kaya ta zauna tsirara.

Somack Aju Mbaise ne ya wallafa wannan labarin mai cike da alhini a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, al'amarin da ya jawo tofin Allah kyauta ga wannan mai aiki.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Shehu Sani ya kara fada wa 'tsaka mai wuya' a hannun hukumar EFCC

Kamar yadda Somack ya wallafa, "wannan wanne irin bakar mugunta ce? Mai aiki 'yar shekaru 16 a duniya ce ta shake 'yar masu gida mai shekaru biyu. A take kuwa yarinyar tace ga garinku. Hakan ta faru ne bayan da mai aikin tayi mata wanka amma taki saka kaya.

"Wannan lamarin ya faru ne a titin Ihechiowa dake kusa da titin MCC a Owerri jihar Imo. Kunga dalilin da yasa ba zan iya daukar mai aiki yarinya ba, zai fi a dauka babba. Kina yin abinda ya saba shari'a in mika ki ga hukuma. Ina fatan kariya daga dukkan sharri." cewar Somack

Kin saka kaya bayan anyi wanka: Mai aiki ta shake 'yar shekaru 2 har lahira

Kin saka kaya bayan anyi wanka: Mai aiki ta shake 'yar shekaru 2 har lahira
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel