Mijina na turawa karuwarshi hotuna na tsirara domin ya muzantani a wajen ta - Matar aure ta koka

Mijina na turawa karuwarshi hotuna na tsirara domin ya muzantani a wajen ta - Matar aure ta koka

- Wata fusatacciyar mata ta rasa yadda zata yi wa mijinta don daukar fansa

- Bayan gama zage-zage da budurwar mijinta a kafar sada zumuntar zamani, sai karuwar ta tura mata hotonta na tsiraici

- Karuwar mijin nata tayi barazanar wallafa hoton a kafar sada zumuntar zamani matukar ta ci gaba da zaginta

Wata mata ta fusata da lamarin mijinta da budurwar shi. Ta wallafa yadda ta gano mijinta ya tura wa budurwar shi hoton tsiraicinta don tozarta ta.

A fada da hargitsin da ya auku tsakanin matar auren da budurwar mijin ta, budurwar mijin tayi barazanar saka hoton tsiraicin matar auren in har ta cigaba da fada mata maganganu bakake. A take kuma ta tura wa matar auren hotunan tsiraicinta wanda ta ce mijin ya tura mata don tozarta matar shi din.

Kamar yadda matar auren ta bayyana "mun fara fada da karuwar mijina a kafar sada zumuntar zamani. Mun zazzagi juna amma sai ta fito min da wata barazana. Hankalina ya tashi kuma rai na ya baci bayan da ta turo min hoton tsiraicina da rubutun da mijina yayi a kai. 'Kalla jikinta, fatar duk babu kyau. Ga wani tumbi da ta ajiye daga haihuwa daya'."

KU KARANTA: A kowanne minti 15 ana yiwa mace 1 fyade a kasar Indiya - Bincike

"Daga bisani ta ce matukar na cigaba da zaginta zata watsa hoton nan a duniya kowa ya gani. Na rasa wanne irin cin mutunci ne wannan. Me zanyi wa mijina in huce mugun takaicin nan"?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel