A kowanne minti 15 ana yiwa mace 1 fyade a kasar Indiya - Bincike

A kowanne minti 15 ana yiwa mace 1 fyade a kasar Indiya - Bincike

- Wata kungiyar kare hakkin mata ta bayyana cewa ba a daukar ta'addancin da aka yi wa mata mataki

- An gano cewa, a 2018 an samu mata da aka yi wa fyade a kasar Indiya sama da 34,000, haka kuma a 2019

- Abin takaicin shine yadda hukumomin da abin ya shafa basu daukar wani mataki

Wata kungiyar kare hakkin mata ta bayyana cewa ba a daukar duk ta'addancin da aka yi wa mata da zafi.

A kowanne minti 15 a kasar Indiya, mace na kai korafin fyade a 2018, kamar yadda kiyasin gwamnati ya bayyana a ranar Alhamis. An gano cewa nan ne wurin da aka fi musgunawa mata a duniya.

Akwai wani fyade da kashe wata mata da aka yi a motar haya a New Delhi a 2012. Lamarin ya jawo zanga-zangar dubban mutane a kan titunan kasar Indiya kuma ya jawo maganganu daga jaruman fim da 'yan siyasar kasar don a dau mummunan matakj a kan lamarin.

An yi wa mata a kalla 34,000 fyade a kasar a 2018 kuma bata sauya zani ba a 2019. An yankewa kashi 27 daga ciki hukunci, kamar yadda rahotan laifuka da ma'aikatar cikin gida ta nuna.

Kungiyar kare hakkin mata ta ce duk laifuka da suka danganci mata ba a daukarsu da muhimmanci kuma 'yan sanda basu bincikarsu.

KU KARANTA: Gwamnati ta gargadi gidajen abinci dake amfani da maganin Paracetamol wajen sarrafa gari

"Har yanzu maza ke mulkar kasar. Alkalai da yawa a kasar maza ne," cewar Lalitha Kumaramangalam, tsohuwar kwamishinar tarayya ta mata.

Fyaden da wani tsohon dan majalisa yayi wa wata matashiya a 2017 ya jawo hankalin mutane saboda wacce aka yi wa fyaden tayi yunkurin kashe kanta sakamakon rashin daukar mataki da 'yan sandan suka yi.

A watanni biyar kafin a yanke wa wanda ake zargin hukunci, dangin matashiyar sun dinga yawo da jami'an tsaro sakamakon yadda tsohon dan majalisar ya dinga harar rayukansu.

A binciken da wata cibiyar shari'a tayi a 2016 a New Delhi, an gano cewa a kan dauka watanni takwas da makonni biyu kafin a kammala shari'ar fyade.

A kiyasin gwamnati, ba a kwashe dukkan fyaden da aka yi a kasar Indiya don wasu yankunan na ganin kai koke a kan fyaden ba daidai bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel