Tashin hankali: Mata tayi yunkurin sayarwa da matsafa dan kamfen karuwar da mijinta ya kawo gidansu

Tashin hankali: Mata tayi yunkurin sayarwa da matsafa dan kamfen karuwar da mijinta ya kawo gidansu

- Ba sabon abu bane idan aka ce mazan aure na bibiyar wasu mata da ba nasu ba a waje

- Wata mata ta fusata da mijin ta bayan ta ga dan kamfai har uku na wata mace a cikin dakin baccinta bayan ta dawo daga hutun sabuwar shekara

- Ta ce tabbas zai amsa tambayoyi amma kuma zata siyar da dan kamfai din ga 'yan damfarar yanar gizo don taji suna amfani dasu wajen asiri

Ba sabon abu bane a ko ina idan aka nuna magidanci kuma ya mallaki wata mace a waje da ya ajiye duk da kuwa yana da mata. Wannan al'adar wasu maza ne, ajiye karuwa don halin ko ta kwana. Wannan kuwa yana ci wa matansu tuwo a kwarya.

Sanannen mai bada shawara a kan zamantakewa, Joro Olumofin ya saba kawo labarai na mata kala-kala. A wannan makon ne ya bayyana labarin wata mata da ta fusata da lamarin cin amana na mijinta. Shi bai tsaya a waje ba, har cikin gidanta kuma a dakin baccinta ta ga alamamomi na yaudara da cin amanar mahaifin 'ya'yanta.

Ta bayyana cewa, bayan tafiya hutun sabuwar shekarar da tayi kuma ta dawo tare da yaran ta biyu, sai ta shirya yin kwalemar gidanta.

KU KARANTA: Tirkashi: Dan siyasa ya bayyana abin da zai yiwa matarshi idan ta nemi yin fada da karuwarshi

Tana cikin sharar ne kuwa taci karo da lamarin da ya tada mata hankali. Dan kamfai din mata ta gani guda uku a cikin bakar leda kulle kuma wadanda ba nata ba. A take ta harde kafa don jiran isowar mijin, don amsa tambayoyi. Amma kuma ta ce zata koyawa karuwar hankali don masu asiri da kamfai din mata zata mika wa. Su yi duk abinda suke so dashi, daga nan kuwa karuwar zata gane kuskurenta na bibiyar mijin wata.

"Mun dawo daga hutun sabuwar shekarar da muka tafi tare da yarana biyu. Sai na yanke hukuncin yin kwalema don tsaftace gidana. A dakin bacci ne kwatsam na ga wata leda baka wacce ban san lokacin da na sharo ta ba. Ina budewa kuwa na ci karo da dan kamfai uku na mata. Cin amana kenan har a cikin dakin bacci na? Yanzu haka jiran shi nake ya zo don amsa tambayoyin da nake dasu. Hakazalika, zan mika dan kamfai din ga 'yan damfarar yanar gizo, don an ce suna asiri dashi. Daga nan karuwar zata gane illar mu'amala da mijin wata." In ji fusatacciyar matar auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel