Tirkashi: Dan siyasa ya bayyana abin da zai yiwa matarshi idan ta nemi yin fada da karuwarshi

Tirkashi: Dan siyasa ya bayyana abin da zai yiwa matarshi idan ta nemi yin fada da karuwarshi

- Wani kwararren mai kiyasi a kan siyasa ya bayyana matakin da zai dauka matukar matar shi ta 'ci zarafin shi' a gaban karuwa

- Olushola ya ce, in har ya taho tare da karuwar shi kuma matar shi ta tozarta karuwar, toh ba shakka ta shirya samun kishiya matukar karuwar bata mayar da martani ba

- Masanin siyasar ya ce hakan ne kadai zai sa ya gamsu da ramuwar gayyar da yake so

Wani kwararren mai kiyasi a kan siyasa ya bayyana tsatsauran matakin da zai dauka a kan matarshi matukar ta tozarta shi ta hanyar wulakanta karuwarshi a gaban jama'a.

Olushola yayi wannan tsokacin ne a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita inda ake bada labarin matar da ta hadu da mijinta da karuwarshi. Amma bata yi kasa a guiwa ba ta nemi tozarta karuwar a kasuwa.

Tsokacin Olushola kuwa ya jawo cece-kuce don wasu sun zargeshi da fifita karuwa a kan matar shi ta sunnah.

KU KARANTA: Tsananin talauci yasa an daure wata mata bayan ta saci akuya ta sayar ta siyawa danta magani

Masanin siyasar dai Olushola ya ce, matukar ya taho a kasuwa tare da karuwar shi kuma matar shi ta gansu, ta kuma nemi tada mishi hankali, toh tabbas zai auri karuwar ne matukar bata daga kai ta kalli tozarcin da matar tashi take mishi ba. Ya ce, hakan ne kadai zai yi don huce takaici.

A kalaman shi, "idan na taho da karuwata a wajen siyayya, kwatsam sai muka ci karo da mata ta kuma ta tozarta ni ta hanyar yi wa karuwar rashin kyautawa, toh ba shakka zan auro karuwar matukar bata mayar wa da mata ta martani ba. Hakan ne kadai zai bani kwanciyar hankali a kan ramuwar gayya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel