Yadda aka dauki bidiyon wata budurwa tana lalata a bainar jama'a bayan ta sha giya ta bugu

Yadda aka dauki bidiyon wata budurwa tana lalata a bainar jama'a bayan ta sha giya ta bugu

- Wani bidiyo na wasu masoya biyu dake lalata a makon da ya gabata a gabar teku ya jawo cece-kuce

- Budurwar da aka aikata wannan abun da ita ta bayyana cewa sharrin giya ce don a bige take

- Budurwar ta ce taji matukar kunyar aukuwar lamarin kuma zata sauya akalar rayuwarta don samun cigaba

Bayan bidiyon wani mutum da suke shakawata da wata mata a gabar teku ya bayyana a wannan makon, an yi ta maganganu a kai. Matar da aka yi wannan bidiyon da ita kuwa ta so a boye ta don fuskarta bata bayyana a wannan bidyon ba.

Amma daga bisani sai ga budurwar ta fito tayi magana. Budurwar ta fito tayi magana a kan illar shaye-shaye mai yawa. Ta ce wannan bidiyon abun kunya ne kuma a shirye take da ta sauya kwata-kwata.

Kamar yadda tace wannan bidiyon na abun kunya ne, ta ce wannan lalata da suka yi ta faru ne sakamakon buguwa da tayi wacce bata taba yin irinta ba.

Ta sanar da Grimsby cewa: “Wannan ba komai bane tunda ba a ga ana lalatar kiri-kiri ba. Nasan illar abinda aka gani yana faruwa da kuma abinda zai iya jawowa. Amma dole ne in cigaba. Giya na da matukar hatsari a don haka ne, bansan abinda ya faru dani ba a mashayar.”

KU KARANTA: Tirkashi: Kamfani na tilasta ma'aikatansa na cin kifi mai rai da kuma shan jinin kaji

Kakakin East Midlands Ambulance Service (EMAS) ta ce: “Ya kamata mutane su kula da kansu a kan shan giya ta wuce misali. Sau da yawa idan aka sha ta da yawa, a kan kasa kula da kai.”

Shugaban Emas, Richard Henderson ya kara da cewa: “Zamu kara yawan ma’aikatanmu a kan titi. Hakazalika zamu fitar da cibiyoyi a wurare daban-daban don rage irin wadannan matsalolin.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel