Bam ya kashe mutane 30 a wata gada mai cike da jama’a a Borno

Bam ya kashe mutane 30 a wata gada mai cike da jama’a a Borno

- Bam ya kashe mutane 30 a wata gada mai cike da jama’a a Borno

- Kamfanin illancin labaran Reuters ta ruwaito cewa bam din ya tashi ne da misalin karfe 5:00 na yamma a gadar da ke cike da mutane a kasuwar garin Gamboru da ya shiga har kasar Kamaru

- An tattaro cewa sama a mutane 35 ne suka jikkata

Akalla mutane 30 ne suka mutu a jihar Borno bayan tashin wani bam da aka dana a kan wata gada, majiyoyi suka fada ma Reuters a ranar Litinin.

Bam din ya tashi ne da misalin karfe 5:00 na yamma a gadar da ke cike da mutane a kasuwar garin Gamboru da ya shiga har kasar Kamaru.

Idanun shaida a kasuwar sun ce an kai sama da mutane 35 da suka jikkata zuwa asibiti biyo bayan harin.

“Ranar bakin ciki ne gare mu yadda muka shaidi wannan mummunan al’amari a garin mu,” inji idon shaida Modu Ali.

“Na ji karar fashewar abu, kafin na ankara sai naka abokaina da abokan harka na da dama sun mutu,” cewar shi.

KU KARANTA KUMA: 2020: Za mu fito da mutane 100m daga cikin talauci – Gwamnatin Tarayya

Majiyoyi biyu na rundunar CJTF sun tabbatar da harin da kuma hasashen yawan mutanen da suka mutu.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin. Daga Boko Haram har ISWAP na kaddamar da ta’addanci a yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel