Imo: ‘Ya ‘yan APC sun ce Ministan ilmi ya na yi wa Jam’iyya makarkashiya

Imo: ‘Ya ‘yan APC sun ce Ministan ilmi ya na yi wa Jam’iyya makarkashiya

APC ta na zargin Chukwuemeka Nwajiuba da zagon-kasa, yayin da ake shiryawa zaben cike-gurbi na Mazabar Isiala Mbano/Onuimo/Okigwe a majalisar tarayya.

Jam’iyyar APC ta jefi Honarabul Chukwuemeka Nwajiuba da zargin yi wa jam’iyya makarkashiya da hada-kai da wata jam’iyya daban da APC da ya ke kai a yanzu.

A cewar wani daga cikin ‘Ya ‘yan APC, Ministan ya na kara samun alaka da jam’iyyar PDP a Imo, wanda wannan ya ke tadawa APC mai hamayya a jihar hankali.

Mataimakin shugaban Matasan APC na jihar Imo, Christogonus Chidi Unezeh, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa Ministan ya na yi wa PDP aiki ta karkashin kasa.

Mista Chidi Unezeh ya ke cewa kusancin Honarabul Nwajiuba da gwamna Emeka Ihedioha, ya jawo ya ke kokarin watsi da zabin da APC ta yi a zaben da za ayi.

KU KARANTA: APC ta fadawa Atiku cewa an daina yayinsa a Najeriya

Imo: ‘Ya ‘yan APC sun ce Ministan ilmi ya na yi wa Jam’iyya makarkashiya
Hon. Chukwuemeka Nwajiuba ya dawo APC ne bayan an yi masa Minista
Asali: UGC

Akwai rade-radin da ke yawo cewa Nwajiuba zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP da zarar kotun koli ta yanke hukunci game da shari’ar zaben gwamnan jihar Imo.

Jagoran jam’iyyar ya cigaba da cewa: “Nwajiuba ya na goyon bayan ‘Dan takarar PDP a zaben da za ayi, a maimakon ‘Dan takarar da jam’iyyarsa APC ta tsaida”

“Tun da aka nada shi Minista, ba a ganinsa wajen taron APC, kuma ba ya bari su hadu da ‘Ya ‘yan APC a jihar Imo, har ma ya na kokarin jan ra’ayin wasu.” Inji sa

Sai dai shugaban APC na Imo, Dan Nwafor ya ce ko da ta tabbata karamin Ministan ba ya halartar taro, ya na nan a APC. Ita kuwa PDP dai ta ce a shirya ta ke ta karbe sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel