Abinda Igbo za suyi don samun shugabancin kasa - Isa Funtua

Abinda Igbo za suyi don samun shugabancin kasa - Isa Funtua

Ismaila Isa Funtua, wani na kusa da shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya zama dole mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya su canja tsarin siyasar su idan dai suna son shugabancin kasa a Najeriya.

Funtua ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar yayin tattaunawa da aka yi da shi wani shiri mai suna The Morning Show a gidan talabijin na Arise.

Uban kungiyan Kungiyoyin masu jaridu ta Najeriya (NPAN) ya ce 'yan kabilar Igbo ba su cakuduwa da sauran yankuna wurin yin siyasa sun fi sun "su ware gefe guda su rika harkokinsu."

Ya ce Moshood Abiola wanda ake ganin shine ya lashe zaben shugaban kasa na 1993 ya yi nasarar kayar da Bashir Tofa ne jiharsa ta Kano saboda ya rungumi kowa.

Funtua ya ce, "Dole su shigo a dama da su. Su shiga jam'iyyun siyasa. Suna son su rika ware kansu don su Igbo ne, su suke mu mika musu shugabancin kasa saboda su igbo ne? Wannan shine dalilin da yasa na ce mulkin Najeriya kamfanin karba-karba ne."

"Ita siyasa batu ne na kuri'u. Abokin na Allah ya jikansa, MKO Abiola ya kayar da Bashir Tofa a Kano. Shin MKO dan Kano ne? Amma ya kayar da Bashir a jiharsa. Mene ne dalili? Saboda mutumin ya yi siyasa, ya rungumi kowa da kowa.

"Idan ka gayyace shi wani taro, idan ba zai samu zuwa ba zai tura wakili. Ba za ka zauna a gefe guda ka ce babu adalci ba saboda kai Igbo ne.

DUBA WANNAN: An kori wata musulma daga wurin aiki saboda ta saka hijabi

"Maganar gaskiya itace idan suka lura yankin kudu maso yamma ba su kusanci shugabancin kasa ba lokacin da suka ware kansu. Kudu maso yamma ta fi kusa da arewa idan kayi la'akari da addini da yanayin rayuwa. Lokacin da Ekwueme ya yi takarar shugaban kasa a PDP, Cif Olusegun Obasanjo ya kayar da shi.

"Na san siyasar Najeriya, kana tsayar da dan takara ne da zai iya kawo maka kuri'u ka ci zabe ba wai addini ko yanki ko kabila ake lura da shi ba. Shin zai zama shugaban Arewa ne, ko Kudu, Ko Yamma?

"Idan Ibo suna son shugabancin kasa, dole sai sun zo an rika dama wa da su. Idan ka ware kanka babu yadda za ayi ka zama shugaban kasa."

Ya kuma zargi wasu kafafen watsa labarai da goyon bayan fafutikan ganin an bawa Igbo shugabancin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel