A Katsina, Yan Shi'a sun yi zaman juyayin kisan Kwamadan Soji Iran da Amurka tayi (Hotuna)

A Katsina, Yan Shi'a sun yi zaman juyayin kisan Kwamadan Soji Iran da Amurka tayi (Hotuna)

Wani babban al'amari da ya dauki hankali duniya yau shine kisan Janar Qasim Sulaimani wanda kasar Amurka ta yi a kan hanya bayan ya dawo daga ta'aziya da safiyar yau Juma'a.

Jama'a suna cigaba da bayyana ra'ayin su kan al'amarin da irin matakin da kasar Iran za ta dauka.

Yan kungiyar mabiya akidar Shi'a a garin Katsina sun yi zaman makoki tare da jajantawa juna kan kisan.

Marigayi Kwamanda Qassem Soleimani ya kasance shugaban rundunar Sojin Iran na wajen kasar.

Hedkwatar Sojin Amurkan ta ce shugaban kasa, Donald Trump, ne ya bada umurnin kashe kwamandojin biyu dake shirin kai hari ofishin jakadancin Amurka a Iraqi.

A Jawabin tace: "Bisa ga umurnin shugaban kasa, hukumar Sojin Amurka ta dauka tsattsaurin mataki wajen yake jami'an Amurka dake waje ta hanyar kisan shugaban rundunar Sojin kwato AlQuds, Qassem Soleimani."

"Soleimani na cikin masu shirye-shiryen kaiwa yan diflomasiyyan Amurka hari a Iraqi."

"Shine ummul haba'isin kisan daruruwan yan Amurka da Sojin gammaya da kuma jikkatan dubunnai."

Kalli hotunan:

A Katsina, Yan Shi'a sun yi zaman juyayin kisan Kwamadan Soji Iran da Amurka (Hotuna)

A Katsina, Yan Shi'a sun yi zaman juyayin kisan Kwamadan Soji Iran da Amurka (Hotuna)
Source: Facebook

Source: Legit

Tags:
Online view pixel