Yanzu-yanzu: Sojoji sun ragargaji yan Boko Haram da suka kai hari Michika

Yanzu-yanzu: Sojoji sun ragargaji yan Boko Haram da suka kai hari Michika

Labarin da ke shigowa da duminsa na nuna cewa dakarun Sojin Najeriya sun fitittiki yan ta'addan Boko Haram da suka kai hari kauyen Ajiri da Michika da yammacin Alhamis, 2 ga watan Disamba, 2019.

Tsohon kakakin hukumar sojin Najeriya, Sani Usman Kukasheka, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Sojojin sun dakile yan ta'addan kuma sun hallaka da dama cikinsu.

Hakazalika ya kara da cewa sun kwace makamai da kayayyaki a hannunsu.

Mun kawo muku rahoton cewa Yan ta'adda Boko Haram na kan kai farmaki karamar hukumar Michika dake jihar Adamawa. The Cable ta bada rahoto

Wani Soja da ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa ya samu kira misalin karfe shida na yamma cewa yan ta'adda sun dira garin.

"Ana kan kai hari Michika yanzu. Sojoji na kan hanyar kawar da su." Ya bayyanawa The Cable

Source: Legit

Tags:
Online view pixel