Najeriya da sauran kasashen duniya 9 da suke da yawan karuwai

Najeriya da sauran kasashen duniya 9 da suke da yawan karuwai

Duk da kasashe da dama na kokarin ganin sun rage yawan mata dake shiga sana'ar karuwanci, har yanzu matsalar na cigaba da yawaita a sassan duniya daban - daban.

Ga jerin kasashen duniya 10 da alkaluman kididdiga suka nuna cewa suna sahun gaba a yawan mata dake sana'ar karuwanci;

10. Kasar Thailand

Kasar Thailand ta haramta karuwanci a hukumance duk da a aikace akwai karuwai a kasar. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata masu sana'ar karuwanci a cikin mutum 10,000.

9. Kasar Jamus (Germanny)

Sabanin sauran kasashen nahiyar Turai, Jamus ta halasta tare da yin tsari ga masu sana'ar karuwanci a kasar. Tun kusan shekarar 1200 AD kasar Jamus ta fitar da tsari ga masu sana'ar karuwanci. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 49 a cikin mutum 10,000.

8. Kasar Malaysia

Kasar Amurka ta yi wa kasar Malaysia bakar lamba a wajen safarar mutane da cin zarafin kananan yara. Watakila hakan ne yasa sana'ar karuwanci ta zama ruwan dare a kasar.

Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 52 a cikin mutum 10,000.

7. Kasar Brazil

Sana'ar karuwanci ba haramun ba ce a hukumance a kasar Brazil, amma kuma doka ta haramta daukan karuwai domin aiki a Otal ko kuma jibge su a wani wuri ba.

Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 53 a cikin mutum 10,000.

6. Kasar China

Kasar China ta haramta sana'ar karuwanci amma ana daukan hakan a matsayin karamin laifi. Wasu masu bincike sun bayyana cewa akwai a kalla mata miliyan 10 dake sana'ar kasuwanci kuma suna taimaka wa kasar wajen samun kudin shiga.

Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 60 a cikin mutum 10,000.

5. Najeriya

Babu wani birni a Najeriya da babu karuwai, kuma sana'ar karuwanci tana kara samun farin jin a Najeriya.

Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 63 a cikin mutum 10,000.

4. Kasar Philippines

Kasar Philippines tana bayar da wata shaida da 'yammata masu sana'ar karuwanci zasu iya rataya wa a wuya domin saukin ganesu, kuma doka ta tilasta musu zuwa gwajin cututtuka da za a iya dauka ta hanyar jima'i (STDs). Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 85 a cikin mutum 10,000.

3. Kasar Peru

Sana'ar karuwanci ta halasta ga 'yammatan da suka kai shekara 18 a kasar Peru matukar sun samu lasisi da takardar gwajin lafiya daga hukuma. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 102 a cikin mutum 10,000.

2. Kasar Koriya ta Kudu

Duk da takunkumin da hukuma ta saka a kan karuwanci da kuma yawan kamen da 'yan sanda ke yi wa karuwai, hakan bai hana karuwai cigaba da harkokinsu ba a kasar Koriya ta Kudu. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 110 a cikin mutum 10,000.

1. Kasar Venezuela

Matsin tattalin arziki ya jawo karuwar yawan masu shiga sana'ar karuwanci a kasar Venezuela, amma, duk da hakan, mafi yawan masu sana'ar karuwanci a kasar bakin haure ne. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 119 a cikin mutum 10,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel