Kimanin Jarirai 26,039 za'a haifa yau, ranar sabuwar shekara a Najeriya - UNICEF

Kimanin Jarirai 26,039 za'a haifa yau, ranar sabuwar shekara a Najeriya - UNICEF

Kwamitin tallafin yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta bayyana cewa sabbin jarirai 26,039 za'a haifa a Najeriya yau ranar sabuwar shekara.

Wakilin UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins, ya bayyana hakan ne a jawabin sabon shekara da ya saki ranar Laraba, 1 ga watan Junairu, 2020.

Mista Hawkins ya bayyana cewa Najeriya ce kasa ta uku a duniya bayan kasar Indiya da Sin, da akafi haifan yara kulli yaumin.

A Indiya, ana haifan yara 67,385 kulli yaumin yayinda ake haifan 46,299 a kasar Sin.

A cewarsa, sabbin jarirai milyan biyu da rabi suka mutu a watansu na farko a shekarar 2018 a duniya.

Yace: "A Najeriya, an samu mutuwa 318,522 cikin yara, yawanci sun mutu ne sakamakon kananan rashin lafiya."

"Bugu da kari, sama da yara milyan 2.5 ke mutuwa kowace shekara, kuma akalla 400,000 aka haifa a mace."

"Ba'a samun kwararrun unguzomomi da zasu rika kula da masu jego da sabbin jarirai kuma sakamakon ba dadi."

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel