Tonon asiri: Ango ya kunna bidiyon amaryarshi a wajen shagalin bikinsu, inda aka ganta tana lalata da wani kato a daki

Tonon asiri: Ango ya kunna bidiyon amaryarshi a wajen shagalin bikinsu, inda aka ganta tana lalata da wani kato a daki

- Wani ango ya tozarta amarayarshi bayan da ya saki bidiyonta tana lalata da mijin kanwarshi

- Ango da amaryar sun sarke da dambe ne bayan da wannan bidiyon ya bayyana, inda ‘yan uwa da abokai suka taso raba su

- An zargi angon da cin zarafin amaryar ne tun kafin aurensu amma ya lallabata ta hanyar yi mata alkawarin gida da mota bayan aurensu

Wani ango ya saki wani bidyo a ranar bikinsu wanda ke bayyana yadda amaryarshi ke cin amanarshi. Wannan bidiyon ya bayyana ne tare da watsuwa a kasar China kuma ya sakeshi ne a gaban ‘yan uwa da abokan arziki yayin shagalin bikin aurensu.

Kamar yadda rahoton yanar gizo ya bayyana, angon ya gane amaryarshi na mu’amala da mijin kanwarshi ne. An gano cewa anyi auren ne a yankin Fujian dake Kudu maso gabas a ranar Alhamis da ta gabata.

A cikin bidiyon an bayyana yadda ma’auratan suka hau kan mumbari a taron bikinsu. Daga nan ne aka fara bayyana bidiyon da ke nuna yadda take kwanciya da mijin ‘yar uwarshi din. A nan ne ya kalleta tare da ce mata: “Kina zaton ban sani bane?”

A take kuwa ta watsa furen dake hannunta a kan mjijin. Daga bisani kuwa sai ‘yan uwa da abokan arziki suka garzayo don raba su. Jaridar Mail Online ta ruwaito.

KU KARANTA: Hotuna: Tayi shigar kamala a Saudiyya, amma ta fidda tsiraicinta a Dubai - Mutane sun kalubalanci Sadiya Kabala

Sauran kananan bidiyon sun kara bayyana amaryar ne da sirikin nata suna lalata.

Wata jaridar kasar China ta bayyana cewa, ma’auratan sun kasance suna soyayya na kusan shekaru biyu kuma an saka ranar bikinsu ne a watanni shida da suka gabata. Angon ya gano cewa amaryarshi na mu’amala da wani ne bayan da yasa naurar daukar rahoto na sirri a gidan da zasu zauna.

Wani ma’abocin amfani da yanar gizo ya yi ikirarin cewa, amaryar ta ci amanar angon nata ne bayan da ya saba da cin zarafinta.

An zargi cewa ta amince ta aureshi ne bayan da yayi mata alkawarin gida da mota bayan aurensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel