Ba na cikin hayyacina a lokacin da na haike wa tsohuwa mai shekara 54 - Matashi

Ba na cikin hayyacina a lokacin da na haike wa tsohuwa mai shekara 54 - Matashi

Laulo Isa, makiyayi dan shekara 20 wanda aka rahoto cewa ya yiwa wata yar shekara 54 fyade, ya bayyana cewa ya aikata laifin ne cikin hali na maye.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan yan sanda sun gurfanar dashi a Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi.

A cewarsa, matar ta zage shi ne inda hakan ya yi sanadiyar fafatawarsu kafin ya yi nasarar shan kanta.

Makiyayin ya kara da cewa baya cikin hayyacinsa a lokacin da ya aikata hakan sannan cewa ya yi danasani matuka kan abunda ya aikata

A ranar 28 ga watan Disamba ne makiyayin ya yiwa wata mata mai suna Misis Mary Okereke fyade har lahira a Ufuezeraku, karamar hukumar Ohaozara.

An tattaro cewa matar na a hanyarta ta dawowa daga gona lokacin da makiyayin ya ci karo da ita, sannan ya ja ta zuwa daji inda ya yi mata fyade har lahira.

Yayinda yake yi mata fyade sai wani mai wicewa ya haska masa fitila sai ya gudu.

Kwamishinan yan sandan jihar, Awotunde Awosola yayinda yake jawabi ga manema labarai kan lamarin ya ce za a hukunta mai laifin kan abunda ya aikata.

KU KARANTA KUMA: Tsohon IGP Idris ya karyata ikirarin shiga siyasar Neja

Mista Awotunde ya ce da taimakon matasaa a garin aka kakkabe jeji da gonakin da ke yankin domin kamo mai laifin.

A cewarsa mai laifin ya bar kayayyakinsa a wajen da lamarin ya afku wanda dashi ne aka gano shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel