Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigaban Afirka, Dakta Akinwumi Adesina, a fadar shugaban kasa Aso Villa yau Talata, 31 ga watan Disamba, 2019.

Hadimin shugaban kasa kan kafafan yada labarai, Buhari Sallau, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.

Kamfanin dilancin labarai NAN ta bayyana cewa shugaban bankin cigaban Afrikan ya isa fadar shugaban kasan ne misalin karfe 11:20 na safe.

Za ku tuna cewa a ranar 21 ga watan Disamba, Akinwumi Adesina ya halarci taron gangamin majalisin tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS inda ya alanta cewa bankin ta taimakawa mutanen nahiyar milyan 18 da wutan lantarki.

Ya kara da cewa bakin ta taimakwa mutane milyan 141 da kayayyakin noman zamani domin tabbatar da koshin lafiya.

Bugu da kari, bankin ta baiwa mutane milyan 13 kudi; mutane milyan 101 hanyar sufuri; da kuma mutane milyan 60 da ruwan sha.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB
Source: Facebook

Source: Legit

Tags:
Online view pixel