Fasto Bakare da Buhari sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa

Fasto Bakare da Buhari sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa

- Fasto Tunde Bakare, Shugaban cocin Latter Rain Assembly a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba ya ziyarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Villa

- Bayan isowarsa fadar shugaban kasa, sai Bakare ya shiga ganawar sirri da Buhari

- Sai dai kuma Bakare ya ki cewa komai game da sakamakon ganawar tasu a lokacin da manema labarai na fadar Shugaban kasa suka tunkare shi, amma ya yi alkawarin dawowa a watan Janairu 2020

Shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba ya ziyarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Da isowar faston birnin tarayya, sai ya shiga ganawar sirri da Shugaban kasar bayan sun dauki hotuna.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa ganawar da aka yi tsakanin shugabannin ya shafe tsawon sama da mintuna 30.

Bakare ya kuma ki cewa komai game da sakamakon ganawar tasu a lokacin da manema labarai na fadar Shugaban kasa suka tunkare shi.

Fasto Bakare da Buhari na cikin ganawar sirri a fadar shugaban kasa

Fasto Bakare da Buhari na cikin ganawar sirri a fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Ya ba da hakuri cewa akwai jirgin da yake saurin samu kafin ya tashi sannan ya yi alkawarin dawowa a watan Janairun 2020.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar dokokin Sokoto ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a majalisa

Bakare ya kasance abokin takarar Buhari a zaben shugaban kasa na 2011 a karkashin jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC).

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel