'Yan sanda sun bankado sabon shirin tarwatsa zaman lafiya a jihar Zamfara

'Yan sanda sun bankado sabon shirin tarwatsa zaman lafiya a jihar Zamfara

Hukumar 'yan sandan jihar Zamfara ta bankado sabon shirin wasu mutane na tarwatsa zaman lafiyar jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.

Yace hukumar tana sanar da mutanen jihar a kan rahoton sirrin da ta samu game da harkokin wasu marasa tausayi kuma masu farin cikin zubar da jinin jama'a da suke samun nishadi wajen yin hakan a jihar.

Wadannan marasa kishin kasar basu farin ciki da zaman lafiyan da ke wanzuwa a jihar a halin yanzu sabooda hakan ya saba wa mummunar bukatarsu.

"A halin yanzu, wadannan mutanen marasa tausayi na ta daukar nauyin miyagun aiyukan da zasu bata sunan jihar a idon sauran garuruwa da kasashen duniya. Hakan a bayyane yake ga hukumar don sun ganosu," in ji SP Shehu .

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da shugaba Buhari ya ziyarta a 2019

Ya ce wannan na kwannan ne ya kasance wani yunkuri da miyagun mutanen suka nuna a kananan hukumomi 14 na jihar bayan da suka raba wasu kudade don daukar nauyin hakan.

"Ta wannan fuskar kuwa, hukumar na kara jaddada cewa babu wani abu da zai sa ta ko sauran hukumomin tsaron jihar ja da baya wajen sauke nauyinsu da kundin tsarin mulkin kasar nan ya dora musu,

"Zasu sauke hakkinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Zasu ci galaba a kan kalubalen tsaro dake addabar jihar a fiye da shekaru 10 da suka shude,

"A halin yanzu ana cigaba da bincike don bankado masu hannu a cikin wannan ta'addancin, kuma za a ladabtar dasu kamar yadda hukuma ta tanada," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel