FG ta amince da bude sabbin kwalejin ilimi a jihohi 6

FG ta amince da bude sabbin kwalejin ilimi a jihohi 6

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin kwalejin ilimi shida a fadin kasar nan. Wannan cigaban ya biyo bayan kokarin gwamnatin tarayya wajen samar da makarantun gaba da sakandire a fadin kasar nan.

Hakan ne ya biyo bayan amincewa wajen kafa sabbin kwalejin ilimin a jihohin da babu su a Najeriya.

Hukumar kulada kwalejin ilimi ta kasa, ta bakin jami'in hulda da jama'arta, ta sanar da cewa za a kafa manyan makarantun a jihohin Bauchi, Benuwe, Ebonyi, Osun, Sokoto da Edo, wadanda babu kwalejin ilimi na tarayya kwata-kwata.

Farfesa Bappa-Aliyu Muhammadu, sakataren hukumar ya jinjinawa kokarin gwamnatin wajen kafa sabbbin kwalejin don cimma bukatar karin malamai a makarantun gwamnati da na kudi a fadin kasar nan. Hakan kuma zai kara inganta ilimi a Najeriya.

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da shugaba Buhari ya ziyarta a 2019

Ya kara da kira ga yankunan da za a kafa sabbin makarantun da su bada goyon bayan da ya dace don fara karatu a sabbin manyan makarantun.

A farkon shekarar nan ne Farfesa Ajiboye ya tsananta kokari wajen tabbatar da hukumar kula da rijistar malamai ta kasa wajen daidaita lamurran malamai a fadin kasar nan. Ya jaddada da cewa akwai bukatar karin malamai a kasar nan don cimma bukatar UNESCO ta yawan malamai ga dalibai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel