Neman kudi: Uwa ta hada-kai da ‘Danta da Malam, an kashe ‘Dalibar Jami’a a Legas

Neman kudi: Uwa ta hada-kai da ‘Danta da Malam, an kashe ‘Dalibar Jami’a a Legas

‘Yan Sanda sun kama wani Mutumi ‘Dan shekara 42 a Duniya wanda ya ke ikirarin cewa shi Malami ne, tare da wasu Bayin Allah, da zargin kashe wata Budurwa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wani Matashi Adeeko Owolabi mai shekara 23 da Mahaifiyarsa Misis Adeeko Owolabi su na cikin wadanda aka kama.

Ana zargin wadannan mutane uku da hannu a mutuwar Favour Daley-Oladele wanda ta kasance Budurwar Owolabi, ta na ajin karshe a Jami’ar LASU da ke Legas.

Marigayiyar da ke karantar ilmin fahimtar dabi’ar mutane ta bar gida ne a Ranar 8 ga Watan Disamba, da nufin za ta je wani wuri, amma ba a sake ganin ta ba.

A dalilin bacewar ta ne Iyayenta su ka kai kara ofishin ‘Yan Sanda da ke Unguwar Moye. Kakakin ‘Yan Sanda na jihar Legas, ya ce daga nan ne aka bazama neman ta.

KU KARANTA: Ta kashe kan ta saboda ta samu sabani da Masoyinta

Babban jami’in ‘Yan Sanda na yankin Mowe, Marvis Jayeola, ya tada Dakaru domin gano inda wannan Budurwa ta shige, a karshe aka samo gawarta a jihar Osun.

Wannan mutum mai ikirarin shi Malami ne mai suna Philip ya shaidawa ‘Yan Sanda cewa Owolabi ne ya kawo Budurwar (Marigayiyar) cocinsa domin ayi tsafi da ita.

Philip. Fasto ne a wani cocin Ikoyi-Ile inda aka samu gawar Budurwar. Saurayin ya fadawa ‘Yan Sanda cewa Malamin ne ya bashi tabarya ya rotsa kan Daley-Oladele.

Bayan ya tarwatsa kan wannan yarinya yayin da ta ke barci, sai ya sa wuka ya yanka wuyanta, ya farke kirjinta, ya dauke zuciyarta, ya kai wa wannan mugun Malami.

Shi kuma Malamin ya hadawa wannan yaro da uwarsa wasu siddabaru daga zuciyar Marigayiyar domin su samu kudi. Yanzu ana cigaba da binciken wannan mugun laifi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel