Ganduje ya nada sabbin masu bashi shawara guda biyar

Ganduje ya nada sabbin masu bashi shawara guda biyar

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdllahi Umar Ganduje, ya amince da nadin sabbin masu bashi shawara na musamman guda biyar.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai a ofishin gwamna, Abba Anwar, ya aika wa kafafen yada labarai a Kano, ya ce nadin masu bayar da shawarar ya fara aiki nan take.

Anwar ya ce gwamna Ganduje ya bukaci sabbin mashawartan da su zage dantse wajen sauke nayin dake rataye a wuyansu tare da yi musu tuni cewa, "zabinku da aka yi daga cikin dumbin jama'a, ya nuna cewa an zabe ku bisa cancanta da kuma kyakyawan zaton cewa zaku kawo wa jihar Kano cigaba."

Wadanda aka nada din da kuma ofisoshinsu sune kamar haka; Hajiya Fatima Abdullahi Dala (mai bayar da shawara a kan harkokin walwalar yara da mata), Dr. Fauziyya Buba (mai bayar da shawara a kan harkokin lafiya), da Hajiya Aishatu Jaafaru (mai bayar da shawara a kan harkar ciyar da dalibai 'yan makaranta).

Ganduje ya nada sabbin masu bashi shawara guda biyar

Ganduje
Source: Depositphotos

Sauran sune; Hajiya Hama Ali Aware (mai bayar da shawara a kan masu saka hannun jari daga kasashen ketare), da Hajiya Yardada Maikano Bichi (mai bayar da shawara a kan harkokin da suka shafi kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs)).

DUBA WANNAN: Disamba: Sabon tsarin karin albashin da gwamnatin Kano ta yi wa ma'aikatanta a matakai daban - daban

A cewar jawabin, "gwamna ya bukaci su kasance masu la'akari da zamani wajen riko da aiyukansu tare da bijiro da abubuwan da zasu kawo wa jihar Kano cigaba domin shiga sahun cikin sauran biranen duniya da suka samu cigaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel