Mayakan Boko Haram sun kone makaranta da coci a sabon harin da suka kai a Borno

Mayakan Boko Haram sun kone makaranta da coci a sabon harin da suka kai a Borno

A daren ranar Lahadi ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari kauyen Mandaragirau dake yankin karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Mayakan kungiyar sun kone Makaranta da Cocin dake kauyen tare da yin awon gaba da wani mutum daya a hanyarsu ta fita daga kauyen.

Jaridar Premium Time ta rawaito cewa mazauna kauyen sun sanar mata cewa babu wani yunkuri ko kokarin dakile harin saboda mayakan sun zo ne da daddare.

Mazauna kauyen da suka shiga gidajensu da wuri saboda yanayin hunturu da ake ciki, sun ranta zuwa cikin jeji yayin da mayakan Boko Haram suka hau harbe - harbe bayan isarsu kauyen.

A cewar wani mazaunin kauyen da ya yi magana da Premium Times, mayakan dake dauke da manyan bindigu sun saka wuta a Coci da Makarantar firamaren kauyen sannan sun jira har saida suka kone kurmus kafin su tafi.

"Sun kone mana makarantar firamare, Coci da sauran wasu shaguna," a cewar majiyar da ta nemi a boye sunanta.

Majiyar ta kara da cewa, "sun yi awon gaba da wani mutum guda daya da suka kama a yayin da yake kokarin neman mafaka."

A cewar majiyar, mazauna kauyen da suka kwana a cikin jejei sun dawo gidajensu da sanyin safiyar ranar Litinin.

Kazalika, tsohon shugaban karamar Biu, Yusuf Adamu, ya tabbatar wa da Premium Times cewa an kai harin a daren ranar Lahadi, kamar yadda majiyar jaridar ta sanar mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel