Yanzu Yanzu: FG ta takaita wa ministoci da wasu zuwa kasashen waje

Yanzu Yanzu: FG ta takaita wa ministoci da wasu zuwa kasashen waje

Ministoci za su iya fita wajen kasar ne sau takwas kacal a shekara, ministan labarai, al’adu da yawon bude ido, Lai Mohammed ya bayyana.

Ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin cewa kada kowani minista da ya tafi kasar waje sama da sau biyu a kwatan zango, jaridar The Nation ta ruwaito.

Bayan nan, kada kowani minista dake ziyarar aiki a kasar waje ya tafi da hadimai wadanda ke da muhimmanci a tafiyar sama da guda hudu.

Daga yanzu jami’an gwamnatin tarayya da ke kasa da mukamin ministoci za su kasance da hadimai kadan. Sannan daga yanzu ba za a dunga lissafin kudin tafiya a kan kowani sa’a ba.

A wani labarin kuma mun ji cewa wata mamba a majalisar wakilai, Honorable Wumi Ogunlola ta yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa majalisar dokoki na tara yan a bi yarima a sha kida ne, inda ta jadadda cewa ba dukkanin bukatun Shugaban kasa Muhammadu Buhari yan majalisar ke yin na’am dashi ba.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar dokokin Sokoto ya mutu bayan ya yanke jiki ya fadi a majalisa

Yar majalisar, wacce ke wakiltan mazabar Ekiti ta tsakiya ta bayyana cewa an zabe su ne domin su yi wakilci domin jama’ar mazabunsu da kuma aiwatar da dokokin da za su kawo gwamnati mai inganci, inda ta kara da cewa ya zama dole dukkanin bangarorin gwamnatin guda biyu su yi aiki cikin aminci domin kasar ta samu dukkanin cigaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel