Atiku Abubakar ya na yunkuri wajen sakin Agba Jalingo daga gidan yari

Atiku Abubakar ya na yunkuri wajen sakin Agba Jalingo daga gidan yari

Tuni ‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fara ganawa da hukumomi wajen ganin an fito da wani ‘Dan jarida da ke tsare a Najeriya.

Alhaji Abubakar ya na ta faman fadi-tashi ne domin ganin Mista Agba Jalingo ya samu ‘yanci. Watanni kimanin hudu kenan, wannan Bawan Allah ya na tsare a gidan yari.

Mai magana da yawun ‘Dan siyasar, Segun Showunmi, shi ne ya kyankyasawa jama’a a shafinsa na Tuwita na @SegunShowunmi cewa Mai gidansa ya na bakin kokarinsa.

Mista Segun Showunmi ya bayyana wannan ne a Ranar Asabar 28 ga Watan Disamban 2019 a dandalin sada zumuntar. Showunmi ya yi Allah-wadai da tsare ‘Dan jaridar.

Hadimin tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ce damke Agba da jami’an tsaro su ka yi abin kunya ne, amma ya ce za su yi abin da ya dace idan kotu sun dawo zama.

KU KARANTA: Atiku ya na iya samun tikitin PDP a zabe mai zuwa

Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ya nuna cewa a shekara mai zuwa ake sa ran Agba Jalingo zai fito daga gidan kurkuku. Yanzu dai sa’anni su ka rage a 2019.

Ana zargin Agba da laifuffuka da-dama wanda su ka hada har da ta’addanci da cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnatin jihar Kuros Riba ta gwamna Ben Ayade.

Alkali mai shari’a Simon Amobeda, shi ne ya ke sauraron wannan kara da aka shigar a Satumban 2019. Jami’an ‘Yan Sanda ne su ka kama Agba a Watan Agusta a Legas.

“Lamarin Agba Jalingo abin takaici ne kuma abin ayi kuka. Ina tabbatar maku da cewa Atiku Abubakar ya na kokarin ganin an cin ma matsaya da zarar an dawo hutu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel