Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

- Shugaba Muhammadu Buhari, a safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, ya yi wata ganawa mai muhimmanci tare da shugabannin tsaro

- Sun yi ganawar ne a fadar shugaban kasa, inda shugabannin tsaron suka koro wa Buhari jawabai

- Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai bai halarci taron ba inda ya samu wakilcin babban jami’in rundunar sojin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, ya yi wata ganawa mai muhimmanci tare da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa.

Anyi ganawar domin Shugaban kasa ya ji bayanai daga shugabannin tsaro ciki hara Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu.

Legit.ng ta fahimci cewa ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ne ya jagoranci shugabannin tsaron zuwa wajen ganawa da Shugaban kasar.

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro
Source: UGC

Shugabannin soji da suka halarci ganawar sun hada da Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar; babban hafsan sojin ruwa, Ibok Ekwe Ibas.

KU KARANTA KUMA: Kisan Kiristoci 11: Ku rike Buhari da Sultan kan ayyukan Boko Haram – Kungiyar dattawan Kirista

Darakta janar na jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, ma ya halarci taron.

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro
Source: UGC

Hakazalika taron ya samu halartan babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da kuma mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno.

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro
Source: UGC

An kuma tattaro cewa Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai bai halarci taron ba. Ya samu wakilcin babban jami’in rundunar sojin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel