Kisan Kiristoci 11: Ku rike Buhari da Sultan kan ayyukan Boko Haram – Kungiyar dattawan Kirista

Kisan Kiristoci 11: Ku rike Buhari da Sultan kan ayyukan Boko Haram – Kungiyar dattawan Kirista

Biyo bayan kisan wasu Kiristoci 11 da aka yi a ranar Kirsimeti, da kuma muzgunawa Kiristoci a wasu yankunan Najeriya, kungiyar attawan Kiristocin kasar (NCEF), ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar za a rike kan habbakan ayyuka da ta’asar yan taddan ISWAP, Boko Haram da kuma makiyaya a kasar.

Hakan na zuwa ne yayinda cigaba da kasancewar Leah Sharibu a hannun yan ta’addan Boko Haram sama da shekara biyu ke kara janyo hankulan mutane a gida da waje, inda suke kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da ganin cewa matashiyar yarinyar bata shiga sabon shekara a hannun yan ta’addan ba.

Shugaban kungiyar ta NCEF, Elder Solomon Asemota, SAN, a wani jawabi ya ce, mayakan ISWAP, wani bangare na Boko Haram ne suka kama Kiristocin guda 11 da lamarin ya cika dasu, inda ya bayyana cewa an nuno mutane 13 a wani bidiyo suna neman ceto inda aka kashe 11.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Sultan na Sokoto yace ya yi mamakin ikirarin kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na cewa ana muzgunawa Kiristoci a kasar.

KU KARANTA KUMA: Zargin bin Yarima a-sha-kida: 'Yar Majalisa ta ce ba zaman Buhari su ke yi ba

Kungiyar ta ce idan har shugaba Buhari ya yarda cewa yan ta’addan sun kasance marasa tsoron Allah, makisa, toh ya yi gaggawan sake fasalin tsaron kasar wanda Musulmai aga arewacin Najeriya ke jan ragamarsa kamar yadda yake a sashi na 14(3) na kunin tsarin mulkin 1999.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel