Tikitin 2023: Atiku ya na kan siradin PDP a takarar Shugaban kasa

Tikitin 2023: Atiku ya na kan siradin PDP a takarar Shugaban kasa

Alamu su na nuna cewa Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ne za su yi dace da samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zabe mai zuwa na 2023.

Wata Majiya daga cikin babbar jam’iyyar hamayyar ce ta bayyanawa Jaridar The Nation wannan. Rahotannin jaridar sun ce ‘Dan takarar PDP zai fito ne daga Arewa ta Gabas.

Kwanakin baya Sanata Walid Jibrin wanda shi ne shugaban majalisar amintattu na jam’iyyar, ya bayyana cewa PDP za ta tsaida matsaya game da yadda za ta tsara zaben 2023.

Wasu ‘Ya ‘yan jam’iyyar su na ganin cewa tun da yanzu shugaban kasa ya fito ne daga Arewa maso Yamma, bai dace a sake tsaida wani ‘dan takara daga yankin a 2023 ba.

A dalilin wannan ne aka fara hangen cewa ana iya zakulo wanda zai rikewa PDP tuta a zabe mai zuwa daga Yankin da Atiku Abubakar ya fito. Amma babu tabbaci game da hakan.

KU KARANTA: Ana iya ba Arewa maso Gabashin Najeriya takarar Shugaban kasa a PDP

A cikin mutum 12 da su ka nemi takarar shugaban kasa a karkashin PDP a 2019, kusan7 sun fito ne daga Arewa maso Yamma. Sauran su ka fito daga tsakiya da gabashin Arewa.

Wani abin damuwa idan har aka kai takarar PDP Arewa maso Gabas shi ne shekaru sun fara ja wajen Atiku Abubakar wanda aka ba tikiti a zaben bana, yanzu shekarunsa 73.

Rabiu Kwankwaso, Attahiru Bafarawa, Sule Lamido, Aminu Waziri Tambuwal, Tanimu Turaki, da irinsu Bukola Saraki da David Mark ba za su yi na’am da wannan shiri ba.

A wani jawabi ta bakin Arinzechukwu Napoleon Igboeli, wanda ke shugabantar wata kungiyar Ibo, Mutanen Kudu maso Gabas ya fi kamata a ba tikitin takara bayan Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel