Kasashe 10 da shugaba Buhari ya ziyarta a 2019

Kasashe 10 da shugaba Buhari ya ziyarta a 2019

Tun daga hawan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada matukar muhimmanci a kan halartar tarurrukan habaka tattalin arziki na duniya. A yayin da wasu ‘yan Najeriya ke kalubalantar wadannan tafiye-tafiyen, suna kuma ganinsu a matsayin na shakatawa ne da yawon bude ido, fadar shugaban kasar ta ce ba haka bane.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, yace shawo kan matsalolin tattalin arzikin Najeriya, na matukar bukatar wadannan tafiye-tafiyen don haduwa tare da karfafa guiwar masu saka hannayen jari don su zo Najeriya.

Shehu ya ce, wadannan tafiye-tafiyen da shugaban kasan yakeyi na bayyana kyawawan sakamako. Legit.ng ta tattara tafiye-tafiye masu matukar muhimmanci zuwa kasashe 10 na shugaban kasa Buhari.

1. Chad

A watan Afirilu ne shugaba Buhari ya ziyarci N’Djamena, babban birnin jamhuriyar Chadi. Shugaban kasar ya je taron shuwagabannin kasashe da gwamnatocin kasashen dake Hamada.

2. Japan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Japan a watan Augusta. Ya je taron habaka Afirka da aka yi a Tokyo. A wannan ziyarar ne ya samu tattaunawa da Firayim Minista Shinzo Abe na Japan.

3. Burkina Faso

A watan satumba ne shugaban kasa Buhari ya garzaya Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso don halartar taron tattalin arziki na kasashen Afirka ta yamma.

DUBA WANNAN: Yadda sojoji da jami'an hukumar kwastam suka ballewa 'yan kasuwa shaguna a Legas

4. USA

A watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je taron UNGA a kasar Amurka. A nan ne ya samu ganawa da wakilan Super Tulcano inda suka tattauna.

5. South Africa

A watan Oktoba ne shugaban kasa Buhari ya ziyarci kasar don taro tsakanin Najeriya da kasar Afirka ta Kudu. A wannan ziyarar ne suka samu tattaunawa a kan harin da ‘yan kasar ke kaiwa bakin haure da suka hada da ‘yan Najeriya.

6. Russia

A watan Oktoba din ne shugaba Buhari ya kai ziyara zuwa wani taron zauren tattalin arziki da aka yi a kasar Rasha.

7. Saudi Arabia

A watan Oktoba ne Buhari ya ziyarci birnin Riyadh don wani taron tattalin arziki. Duk da cewa kuwa a watan Mayu ne sarki Salman Bin Abdulaziz ya gayyaci Shugaba Buhari don yi Umrah.

8. Landan

A watan Nuwamba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Birnin Landan don hutawarsa ta makonni biyu.

9. Equatorial Guinea

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Equitorial Guinea don taro a kan iskar Gas. Sauran shuwagabannin kasashe masu samar da iskar gas duk sun halarci taron.

10. Egypt

A watan Disamba ne shugaba Buhari ya kai ziyara kasar Egypt don taron zaman lafiya da habaka Afirka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel