‘Yan Sanda za su daina gurfanar da masu laifi a kotu – Gwamnatin Kano

‘Yan Sanda za su daina gurfanar da masu laifi a kotu – Gwamnatin Kano

Nan gaba Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya za su rasa ikon gurfanar da wanda aka samu da zargin aikata laifi a gaban kotun da ke jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bada wannan sanarwa a Ranar Lahadi, 29 ga Watan Disamba, 2019, ta bakin Kwamishinan shari’a, Ibrahim Mukhtar.

Ibrahim Mukhtar wanda shi ne babban Lauyan gwamnatin jihar Kano ya bayyana cewa an yi wa dokokin jihar Kano wasu kwaskwarima.

Mukhtar ya ce an kawo wadannan cigaba a harkar dokokin laifuffuka ne domin karfafa bangaren shari’a, kamar yadda mu ka samu labari.

A cewarsa, gwamnatin ta dogara ne da sashe na 221 na kundin tsarin mulki wajen haramtawa ‘Yan sanda shigar da kara a madadin jihar.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi wa CAN raddi kan zargin matsawa Kiristoci

‘Yan Sanda za su daina gurfanar da masu laifi a kotu – Gwamnatin Kano

Za a rika gabatar da kwararrun Lauyoyi wajen tuhumar mai laifi a Kano
Source: Facebook

Haka zalika Kwamishinan ya ce sun yi la’akari da sabuwar dokar laifuffuka a kokarin su na yi wa ayyukan ‘Yan Sandan kasar garambawul.

“Mu na kokarin karbe gaba daya sha’anin gurfanar da Mai laifi a gaban kotu daga hannun ‘Yan Sanda a jihar.” Inji Hon. Ibrahim Mukhtar

Kwamishinan ya ce: “Tun da aikin ‘Yan Sanda ya kunshi gano laifi da bincike da hana laifuffuka, za mu taimaka masu wajen wannan aiki."

“Sai ka ga cewa Masu laifi su na damar daukar hayar har manyan Lauyoyi na SAN yayin da hukuma ta dogara da Lauyoyin ‘Yan Sanda.”

Kwamishinan ya ke cewa Lauyoyi da ke tsayawa gwamnati su na da karancin ilmi don haka su ke neman ganin an gyara wannan lamari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel