Yadda sojoji da jami'an hukumar kwastam suka ballewa 'yan kasuwa shaguna a Legas

Yadda sojoji da jami'an hukumar kwastam suka ballewa 'yan kasuwa shaguna a Legas

- Kamar yadda majiya da dama suka sanar, jami'an hukumar kwastam da sojoji sun kai samame kasuwar Yaba dake Legas

- Sun balle shagunan 'yan kasuwa inda suka kwashe duk kayan gwanjon dake shagunan 'yan kasuwar

- Lamarin ya faru ne a ranar 29 ga watan Disamba 2019 ne lokacin da 'yan kasuwar suka tafi hutun Kirsimeti

Kamar yadda majiyoyi masu yawa suka tabbatar, jami’an kwastam din Najeriya da sojojin Najeriya an zargesu da kai samame a ga wasu shaguna a Yaba, Legas.

An zargesu da balle shagunan ne inda suka kwashe kayan gwanjon da ‘yan kasuwar ke siyarwa.

Lamarin ya faru ne a ranar 29 ga watan Disamba, 2019. Sun balle wa ‘yan kasuwar shagunansu tare da kwashe kayan siyarwarsu ne bayan da suka tafi hutun Kirsimeti.

DUBA WANNAN: Cunkuson Apapa: Dangote ya yi asarar biliyan N25 a cikin shekara biyu

Kamar yadda kafafen sada zumuntar zamani suka dinga sanarwa, jami’an sun kwace kayayyakin gwanjo ne wadanda jami’an ke zargin cewa an shigo dasu ne daga kasashen ketare.

Ga yadda wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ya ruwaito: “kalli abinda ke aukuwa a Yaba na jihar Legas. A titin Popo ne jami’an hukumar kwastam suka kai samem zuwa shagunan da ake siyarda gwanjo. Sun balle shagunan tare da fito da kayan gwanjon. Sun tafi dasu da safiyar yau ta ranar 29 ga watan Disamba 2019.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel