Masu garkuwa sun dauke mutum 3 a Katsina tare da tarin dabbobi a jahar Katsina

Masu garkuwa sun dauke mutum 3 a Katsina tare da tarin dabbobi a jahar Katsina

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kauyuka guda hudu dake cikin karamar hukumar Dutsanman jahar Katsina, inda suka sace mutane uku tare da awon gaba da shanu da dama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da mutane biyu a kauyen Maitsani da suka hada da Sale Rahama da Bilkisu Sunusi, sa’annan suka dauke Alhaji Bello Suke a kauyen Darawa.

KU KARANTA: Jerin wasu zafafan wakokin Hausa 10 da suka burge jama’a a cikin shekarar 2019

Yayin da a kauyen Madagu kuwa suka tattara shanu 60 da tumaki 40, haka zalika sun kwashe dabbobi da dama daga kauyen Gefen Kubewa, duk a cikin karamar hukumar Dutsanma, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kai harin ne da tsakar daren Asabar, 28 ga watan Disamba, inda suka kwashe tsawon sa’o’i sun tafka tsiyarsu. Mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan bindigan sun matsa musu a tsawon mako daya da ya gabata, kuma a duk hari sai sun kashe rai ko su sace mutum.

Shi ma mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da kai harin, sai dai yace tuni an tura Yansandan SARS da na Puff Adder zuwa yankin domin yakar yan bindigan dake labe a yankin.

Jahar Katsina na daya daga cikin jahohin da ayyukan yan bindiga masu garkuwa dsa mutane ke cigaba da ta’azzara a yankin Arewacin Najeriya, inda a yanzu haka jahar ta sha gaban jahohin Zamfara da Kaduna wajen samun yawaitar hare haren.

Amma gwamnatin jahar Katsina ta bullo da shirin yin afuwa ga miyagun domin samun sulhu tare da tabbatar da zaman lafiya, ta yadda idan suka sako mutanen dake hannunsu, sai gwamnati ta yafe musu laifukansu ba tare da tuhume su ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel