Nasarawa: Tsofaffin ‘Ya ‘yan APGA da PDP sun dawo jirgin APC a Wakama

Nasarawa: Tsofaffin ‘Ya ‘yan APGA da PDP sun dawo jirgin APC a Wakama

Sama da mutum 1, 000 ne daga jam’iyyun PDP da APGA da sauran jam’iyyun hamayya su ka sauya-sheka zuwa APC mai mulki a Garin Wakama da ke jihar Nasarawa.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 29 ga Watan Disamba, 2019, wadanda su ka dawo jam’iyyar APC sun hada da tsofaffin Kansiloli da shugabannin jam’iyya.

Haka zalika wasu tsofaffin Sakatarorin jam’iyyar PDP sun tsere daga jam’iyyar zuwa APC a Mazabar Wakama da ke Nasarawa a karshen makon nan da ya gabata.

Ma’ajin jam’iyyar APC, Mohammed Aya, shi ne ya karbi sababbin shigowa APC a Garin na Wakama a jiya Ranar Lahadi a wani biki da aka shirya na musamman.

Mohammed Aya ya wakilici shugaban jam’iyyar APC na Nasarawa watau Philip Shakwo wajen tarbar wadannan dinbin ‘Yan siyasa zuwa cikin tafiyarsu ta APC mai-ci.

KU KARANTA: Ana cigaba da rikici tsakanin Jiga-jigan APC a Jihar Edo

Nasarawa: Tsofaffin ‘Ya ‘yan APGA da PDP sun dawo jirgin APC a Wakama

Silas Agara da wasu 'Yan Majalisa sun karbi tsofaffin 'Yan PDP
Source: UGC

Mista Philip Shakwo ya shaidawa bakin cewa su na da duk wata dama da kowane tsohon ‘Dan jam’iyya ya ke da ita a tafiyar siyasa, bayan wannan sauyin-sheka da su ka yi.

Shugaban jam’iyyar, ta bakin Ma’ajinsa na jihar, ya kuma shaidawa tsofaffin ‘Yan adawan cewa gwamnati za ta kai ayyuka yankinsu a matsayin tukwuicin yaba alherinsu.

Tsohon mataimakin gwamna, Silas Agara, ya kara tabbatarwa mutanen Yankin na Wakama cewa ayyuka za su kai gare su nan gaba tun da sun zabi su bi jirgin APC.

Bala John shi ne ya yi magana a madadin sauran sababbin Magoya bayan na APC inda ya ce sun sauya-sheka ne saboda cigaban yankinsu ganin kokarin gwamnatin APC.

“Wakama ne kadai Kauyen da gwamnatin tarayya ta ke yin hanyoyin kilomita 6.” Irin wannan aiki na gwamnatin Buhari da ta jihar Nasarawa ya jawo dinbin mutanen.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel