Shehu Sani: Ka da ‘Yan Najeriya su sa ran ganin wani canji a shekarar 2020

Shehu Sani: Ka da ‘Yan Najeriya su sa ran ganin wani canji a shekarar 2020

Sanata Shehu Sani ya yi gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ya ke jagoranta kaca-kaca, inda ya fadawa jama’a ka da su sa ran ganin wani canji daga shekarar badi.

Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan da ta shude, ya bayyana cewa wahalar da ‘Yan Najeriya su ke fuskanta zai karu ne a shekarar badi.

‘Dan siyasar ya bayyana wannan ne a Ranar Lahadi, 29 ga Disamban 2019, a lokacin da aka gayyace sa shirin ‘Kai kadai gayya’ a gidan rediyon Invicta FM a Kaduna.

A wannan shiri na Hausa da aka yi, Shehu Sani ya bayyana cewa ko da wannan gwamnati mai-ci za ta shafe shekaru 50 a mulki, ba za ta kawo wani abin kirki a kasar nan ba.

Kwamred Sani ya zargi shugabannin da ke mulki a yanzu da daura laifi a kan gwamnatocin baya, a maimakon su kama hanyar gyara kasar daga yadda su ka karbi ragamarta.

KU KARANTA: 2023: Sanatoci 2 da Gwamna 1 sun fara harin ajiye siyasa a Najeriya

Shehu Sani: Ka da ‘Yan Najeriya su sa ran ganin wani canji a shekarar 2020

Sani ya ce wuyar da 'Yan Najeriya su ke sha za ta karu daga badi
Source: UGC

Shehu Sani ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su yi kokari wajen ganin ragargaji romon damukaradiyya a karshen wannan gwamnati tare da sukar matakan da gwamnatin ta dauka.

Sanatan ya ke cewa muradun wannan gwamnati za ta sa jama’a su kara shiga cikin halin wahala ne a nan gaba, inda ya fito gar-da-gar ya soki batun garkame iyakokin kasar.

Fitaccen ‘Dan gwagwarmyar ya ce majalisar baya ta yi fatali da batun rufe iyakoki a lokacin da aka fara tado maganar a shekarun da su ka wuce domin bai da wani iamfani.

A cewar Sanata, rufe iyakokin bai karawa tattalin arzikin kasar komai ba sai karin talauci ga marasa arziki. A karshe ya ce da jami’an tsaro ake lashe zabe a Najeriya a yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel