Farawa da iyawa: Za’a gudanar da zanga zangar kin jinin Oshiomole a 2020

Farawa da iyawa: Za’a gudanar da zanga zangar kin jinin Oshiomole a 2020

Wani babban jigo a tsakanin shuwagabannin jam’iyyar APC mai mulki zai shirya gangamin zanga zangar neman ganin an kawar da kwamared Adams Oshiomole a matsayin shuhgaban jam’iyyar APC na kasa.

Jigon mai suna Kabiru Adjoto ya bayyana cewa zai gudanar da wannan gangamin zanga zangar ne a farkon shekarar 2020 domin bayyana bacin ransa da salon kamun ludayin mulkin Oshiomole, wanda yace ya janyo rarrabuwai kai a cikin jam’iyyar.

KU KARANTA: Jerin wasu zafafafn wakokin Hausa 10 da suka burge jama’a a cikin shekarar 2019

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Kabiru ya bayyana haka ne a garin Igarralan jahar Edo inda yace: “Ina shirin gudanar da gangamin tsige Oshiomole a firkon watan Janairun shekarar 2020 a jahohin Najeriya 36, ba zamu sassauta ba har sai Oshiomole ya sauka.”

Kabiru, wanda tsohon kaakakin majalisar dokokin jahar Edo ne, kuma a yanzu hadimin gwamnan jahar, Godwin Obaseki, yace zai yi tone tonen asirce asircen da zasu kawo karshen siyasar Oshiomole a Edo, ta yadda idan jama’a sun gan shi zasu yi masa jifar shedan.

Idan za’a tuna an yi ta samun takun saka tsakanin Oshiomole da Obaseki tun lokacin da zaben gwamnan jahar Edo ya fara karatowa wanda ake sa ran gudana a watan Agustan shekarar 2020, kuma duk kokarin da aka yi na sulhunta giwayen siyasar biyu hakan ya ci tura.

A wani labarin kuma, tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon sakataren jam’iyyar CPC, Alhaji Buba Galadima ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.

Jaridar Blueprint ta ruwaito Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da gidan jaridar Daily Independent, inda yace idan har shugaba Buhari ya cika masa burinsa, ba zai bukaci kudi daga gwamnatin tarayya kafin ya shirya zabe ba.

Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake caccakar shugaban hukumar mai ci, Farfesa Mahmud Yakubu, inda ya zarge shi da hada kai da hukumomin tsaro wajen kayar da jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel