Adojoto: Shugaban Jam’iyya Oshiomhole ya gamu da barazana a Jihar Edo

Adojoto: Shugaban Jam’iyya Oshiomhole ya gamu da barazana a Jihar Edo

Sa’o’i kadan ga sabuwar shekara, Daily Trust ta fahimci cewa rigingimu su na cigaba da aukowa shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya, Adams Oshiomhole.

A Ranar Lahadin da ta wuce, wani daga cikin Jiga-jiga jam’iyyar APC, Alhaji Kabiru Adjoto, ya zari takobin shirya zanga-zanga domin ayi waje da shugaban jam’iyyar.

A jawabin da Kabiru Adjoto ya yi a Ranar 29 ga Watan Disamba, 2019, ya nuna cewa za a gudanar da wannan zanga-zangar ‘A yi waje da Oshiomhole’ ne a fadin kasar.

“Zan shirya gagarumin zangar-zangar yi wa Oshiomhole bore, wanda za a fara a farkon shekara mai zuwa da dinbin Mabiya cikin duka jihohi 36 na fadin kasar nan.”

Adjoto wanda tsohon Kakakin majalisar dokokin Edo ne, ya shaidawa ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC wannan ne a Kauyensa na Ikakumo da ke cikin Igarara a jihar Edo.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar PDP zai kawa cikas wajen wani burin da aka sa gaba

Tsohon ‘dan majalisar ya ce: “Ba za a dakatar da wannan zanga-zanga ba har sai Oshiomhole ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyya kafin ya kai APC ga halaka.

“Kamar yadda na yi alkawari a baya, na fada a shirye na ke in fasa kwan da zai sa jama’a su rika jifar Oshiomhole a gari a yayin da aka shiga wata sabuwar shekara.”

Alhaji Adjoto bai iya bayyanawa ‘Yan jarida abin da zai bankado da zai sa jama’a su juyawa tsohon gwamnan baya ba. Amma ya karyata jita-jitar sauya shekar gwamna.

Yanzu haka Adjoto wanda ya na cikin Masu ba gwamna Godwin Obaseki shawara, ya bayyana cewa maganar cewa gwamnan zai koma PDP sam ba gaskiya ba ne.

“Oshiomhole zai bizne kansa a siyasa har abada saboda hadama da munafunci." A cewarsa, Oshiomhole ya na kokarin komawa Ubangida, abin da ya yaka a da.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel