Wani ‘Dan Majalisar Ekiti ba ya goyon bayan kashe N37b a Najeriya

Wani ‘Dan Majalisar Ekiti ba ya goyon bayan kashe N37b a Najeriya

Wani ‘dan majalisar wakilan tarayya Honarabul Bamidele Salam, ya nuna rashin goyon kashe biliyoyi wajen yi wa majalisa kwaskwarima.

Bamidele Salam ya bayyana cewa zai fi kyau a ware N100, 000 wajen ba mutane 370, 000 bashin jarin kasuwanci da za su biya daga baya.

Honarabul Salam ya fito da ra’ayinsa a fili ne a wani jawabi da ya yi a shafinsa na sada zumunta a Ranar Lahadin nan 29 ga Disamban 2019.

“Ni ‘Dan Majalisa ne amma gaskiya ba na goyon bayan cewa mu na bukatar kashe Naira biliyan 37 wajen gyara wannan majalisar.” Inji sa.

‘Dan majalisar ya ce: “A matsayi nan a mai rajin bunkasa tattalin arziki domin samar da aikin yi, gara in ga an ba 'Yan kasuwa 370, 000 jari...”

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya bayyana lokacin da zai yi ritaya daga siyasa

Wani ‘Dan Majalisar Ekiti ba ya goyon bayan kashe N37b a Najeriya

Ana neman kashe Biliyan 37 domin yi wa Majalisa 'yan gyare-gyare
Source: Twitter

Jawabin ‘dan majalisar tarayyar kasar ya cigaba da cewa: “…kudi N100, 000 da babu ruwa wanda za a biya daga baya cikin shekara guda.”

“Bayan gyaran kayan na’ura da daukar sautin da ake amfani da su, daukacin ginin majalisar ba ya bukatar gyaran da ya wuce wanda makarantu da asibitoci da titunanmu su ke bukata.”

“Idan mu ka tattaro gaba daya kudin da za a kashe wajen gyara fadar shugaban kasa da sauran ofisoshin ‘Yan siyasa da jami’an gwamnati, za mu samu rubu’in Naira tiriliyan daya.”

'Dan majalisar adawar na jihar Ekiti ya na ganin cewa wannan kudi har Naira biliyan 250 za su isa a bunkasa kananan kasuwanci a shekara mai zuwa.

“Da yardar Ubangiji, idan an dawo zama a Watan Junairu, zan fara wannan fafatuka a zauren majalisa.

“Ba a taba makara wajen aikin alheri.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel