Masari ya sanar da ranar da zai yi murabus daga harkokin siyasa

Masari ya sanar da ranar da zai yi murabus daga harkokin siyasa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya bayyana cewa yana shirin yin murabus daga harkokin siyasa da zarar wa'adin zangon mulkinsa na biyu ya kare a shekarar 2023.

A yayin hirarsa da jaridar Daily Trust a ranar Lahadi, Masari ya bayyana cewa zai cika shekaru 73 a lokacin da zai zama zangonsa na biyu a matsayin gwamna, a saboda haka akwai bukatar ya huta saboda tsufa ya kama shi.

"Zan yi murabus daga siyasa da zarar na bar ofis a shekarar 2023, lokacin zan cika shekara 73 a duniya, ina bukatar hutu kuma a wannan lokacin. Zan koma bayan fage," a cewar Masari.

Kafin ya zama gwamna a karo na farko a shekarar 2015, Masari ya rike mukamin shugaban majalisar wakilan Najeriya na tsawon shekara hudu, daga 2007 zuwa 2011.

Masari ya sanar da ranar da zai yi murabus daga harkokin siyasa

Aminu Bello Masari
Source: UGC

Yanzu haka Masari yana cin zangonsa na biyu ne a matsayin gwamnan jihar Katsina bayan ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Katsina da aka gudanar a farkon shekarar 2019.

DUBA WANNAN: APC: Manyan 'yan siyasa 5 da zasu iya taimakon Tinubu ya cimma burinsa a 2023

A kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Gombe, sanata Danjuma Goje, ya bayyana cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa tare da fadin cewa ba zai kara fito wa takarar neman wata kujera ba a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel