Masarautar Kano: Jan aikin da ke gaban Kwamitin Janar Abdussalami

Masarautar Kano: Jan aikin da ke gaban Kwamitin Janar Abdussalami

Jaridar Daily Trust ta yi bincike game da yadda rikicin masarautar Kano ta ci wasu manyan masu rike da sarautar kasar Kano. Daga ciki har da masu ikon nada Sarki a kasar.

Wadanda wannan sabani na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi ya shafi Masu nada Sarki 4, Hakimai 14 da kuma manyan Mukarraban Sarki uku.

Sarkin Ban Kano, Hakimin Danbatta, Alhaji Adnan Mukhtar, ya fada karkashin sabon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero. Kwanaki ya rasa kujerarsa saboda rashin yin biyayya.

Adnan Mukhtar ya na kan kujerar Danbatta tun a 1954 kuma ya na cikin masu nada Sarki a Kano tun tuni. An tsige sa daga gadon sarauta a dalilin kin yi wa Sarkin Bichi mubaya’a.

Masu nada Sarkin da su ke rikici da sababbin Sarakunan da aka nada su ne: Alhaji Yusuf Naba-hani, Abdullahi Sarki Ibrahim, da Alhaji Bello Abubakar da kuma Mukhtar Adnan.

KU KARANTA: Manyan 'Yan siyasan da za su taimakawa Bola Tinubu a 2023

Wadannan masu nada Sarki su ne ke rike da sarautar Madakin Kano, Makaman Kano, da Sarkin Dawaki Maituta da kuma Sarkin Bai wanda su ka kai gwamnatin jihar Kano kara.

Madakin Kano Nabahani da Sarkin Ban Kano su ne aka tsige a Kasar Bichi. Sauran wadanda aka tunbuke daga gado su ne: Barden Kano, Hakimin Tsanyawa da Hakimin Minjibir.

Haka zalika a dalilin wannan rikici, Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulqadir Gaya, ya tunbuke Makaman Kano, Sarki Ibrahim, da Sarkin Dawaki Maituta, I. Abubakar daga Hakimci

Rikicin Masarautar ya ci Hakiman Rimingado da Kiru. A kasar Karaye, an kori Hakiman Kura da Dankadan Kano. An kuma tsige Hakimai a Bebeji, Doguwa, Garun Malam da Takai.

Hadiman Sarkin Birni Muhammadu Sanusi II da aka tsige a dalilin rigimar su ne Alhaji Isa Pilot da Alhaji Auwalu Idi wanda shi ne Majasirdin Kano da kuma Sokon Sarkin Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel