Dole a kamo kuma a hukunta wadanda suka kai mini hari gidana - Jonathan

Dole a kamo kuma a hukunta wadanda suka kai mini hari gidana - Jonathan

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci hukumomin tsaro da su bankado tare da ladabtar da wadanda suka kai mishi hari har gida

- Ya mika godiyarshi ga 'yan Najeriya, shuwagabanni da magoya bayanshi da suka jajanta mishi aukuwar lamarin

- Kamar yadda yace, ya samu ziyara da kiraye-kiraye daga shugaban kasa, gwamnoni da 'yan siyasa don jaje

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan yayi kira da a bankado tare da hukunta 'yan bindigar da suka hari gidanshi a Otueke, jihar Bayelsa.

Ya kara da yin godiya ga 'yan Najeriya game da kara da jaje da suka yi mishi sakamakon harin da aka kai a jajiberin Kirsimeti har gidanshi.

Tsohon shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin da ya riski masu jajen a wajen da abun ya faru. Ya kara da jinjinawa sojin Najeriya da suka nuna sadaukantakarsu wajen fatattakar 'yan bindigar amma duk da haka sai da aka rasa ran soja daya.

Jonathan yace tun da aka kai harin a ranar 24 ga watan Disamba, 'yan Najeriya masu fadi a ji kamarsu shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnonin jihohi da shuwagabannin jam'iyyun siyasa suke kai mishi ziyara ko kuma kiranshi don jajanta mishi.

KU KARANTA: Hotuna: 'Yan fashi sun ga ta kansu a Abuja, yayin da sojoji suka hana su guduwa bayan sun gama fashi a banki

Ya kara jaddada kiranshi ga hukumomin tsaron da abun ya shafa da su bankado tare da tabbatar da an ladabtar dasu.

A ranar 24 ga watan Disamba ne wasu 'yan bindiga suka hari gidan tsohon shugaban kasa Jonathan dake Otueke. Sun isa ne wajen karfe 1:30 na ranar Talata. Bayan musayar wuta da ta shiga tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro dake shingen kafin isa gidan Jonathan din, sun halaka soja daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel