Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram da ke kokarin karbe wani gari a Adamawa

Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram da ke kokarin karbe wani gari a Adamawa

- Rahotanni sun ce 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram na kokarin karbe wani gari a jihar Adamawa

- Sai dai, dakarun sojojin Najeriya suna fafatawa da su domin ganin ba su ci nasarar karbe garin ba

- Wannan harin na zuwa ne kimanin mako guda bayan sojojin sun dakile wata harin da 'yan ta'addan suka kai a jihar

Rahoton da Sahara Reporters ta wallafa na nuna cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram a halin yanzu suna kokarin karbe garin Madagali da ke jihar Adamawa.

Legit.ng ta tattaro cewa wani mazaunin garin ne Madagali ne ya kira kafar yadda labarin na yanar gizo a wayar tarho inda ya sanar da su abinda ke faruwa kuma ana iya jin karar harbin bindiga a garin.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

A cewar rahoton, dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi kokarin fattatar 'yan ta'addan domin hana su shigowa garin na Madagali.

Rahoton ya nuna cewa kimamin mako guda da ya wuce sojojin na Najeriya sun dakile wata hari da 'yan ta'addan suka kai a garin.

A halin yanzu dai babu cikakken bayani a kan rasa rayuka ko dukiyoyi sakamakon artabun da sojojin ke yi da 'yan ta'addan a lokacin rubuta wannan rahoton.

An gano cewar shugaban hafsin sojojin Najeriya, Laftant Janar Tukur Buratai zai kai ziyara garin na Adamawa a gobe Lahadi 20 ga watan Disamban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel