Masu garkuwa sun sace wani ya tafi biyan kudin fansa a Katsina

Masu garkuwa sun sace wani ya tafi biyan kudin fansa a Katsina

Masu garkuwa da mutane, a jiya Juma'a sunyi garkuwa da wani mutum mai matsakaicin shekaru, Ibrahim Lukman yayin da ya tafi kai musu kudin fansar 'yar uwarsa, Aisha da su kayi garkuwa da ita.

An sace Aisha ne makonni biyu da suka gabata a gidan mijinta da ke kauyen Dangani a karamar hukumar Musawa a wani hari da suka kai inda suka raunta mai gidanta da ke jinya yanzu a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Katsina.

Wata majiya ta ce masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da Aisha bayan kai harin kuma suka nemi a biya naira miliyan 1.5 a matsayin kudin fansarta.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

Ibrahim ya amince cewa zai hadu da masu garkuwa da mutanen dauke da kudin da suka bukata a kusa da dajin Yantukami inda suka dauke shi a kan babur domin su kai shi inda suka ajiye 'yar uwansa.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya ce rundunar ta sha gargadin mutane su dena tattaunawa da masu garkuwa da mutane a kan kansu.

Ya ce, 'yan sanda suna gudanar da aikinsu cikin gaskiya da jarumta inda ya ce, "abin takaici ne yadda wasu mutane suka zagawa su rika tattaunawa da masu garkuwa da mutane, munyi bakin cikin jin cewa 'yan uwan wanda aka sace sun tafi daji domin biyan kudin fansa, ba mu son mutane su rika tattaunawa da miyagu."

Kazalika, a jiya wasu 'yan bindiga sun sace wata matar aure, Amina Usman a gidan ta da ke kalon masallacin Idi na 'yan Izala a garin Dutsinma.

Masu garkuwar sun raunata mijinta yayin harin kuma a halin yanzu yana babban asibiti garin yana jinya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel