Yadda budurwa ta kashe tsohon masoyinta kwanaki kadan kafin daurin aurensa

Yadda budurwa ta kashe tsohon masoyinta kwanaki kadan kafin daurin aurensa

'Yan sanda sun tsare wata malamar makaranta firmare ta kudi a jihar Legas, Jacinta Igboke kan zargin kashe tsohon masoyinta, Arinze Ani.

Igboke da dabawa Ani wuka ne da ya yi sanadin mutuwarsa a ranar Talata sakamakon rashin jituwa da suka samu a shagonsa da ke tsohon layin Ojo a jihar ta Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.

City Round ta gano cewa Ani da ke sana'ar sayar da sabulu yana shirin auren wata mata a ranar 4 ga watan Janairun 2020 bayan soyayyarsu da Igboke ta rushe duk da cewa sun haifi da daya da yanzu ke da watanni 18 da haihuwa.

An gano cewa soyayyar ta su da suka fara tun 2016 ta samu matsala ne jim kadan bayan Igboke ta dauki ciki.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

Tsautsayin ya afku ne a ranar Talata yayin da malamar ta tafi shagon Ani domin ta karba kudin kulawa da dan su amma hakan ya haifar da musu tsakaninsu wadda haka ya sa Igboke da daba wa Ani wuka a kirjinsa.

Matar mai shekaru 29 'yar asalin jihar Ebonyi ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa iyayen Ani sun ce ba za ta aure shi ba saboda ta girme shi kuma suna son ya auri mata daga kauyensu a jihar Enugu kafin 'yan sanda su tafi da ita.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Bala Elkana ya ce za a tafi da wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike.

Ya ce, "An sanar da mu cewa wata mata da dabawa saurayinta wuka a barin dama na kirjinsa kuma haka ya yi sanadin mutuwarsa. Tawagar 'yan sanda sun isa wurin kuma suka ceto matar daga hannun fusatattun mutane kuma aka dauko gawar mammacin.

"An tafi da gawar mammacin zuwa asibiti domin gudanar da bincike. Wanda ake zargi da wanda aka kashe masoya ne kuma suna da da namiji guda daya wanda ya kai kimanin shekara daya da rabi da ake kyautata zaton batun kulawa da shi ne ya janyo rikici tsakaninsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel