Tashin hankali: Dan Acaba yayi hadari ya mutu ya bar mata 6 da 'ya'ya 30

Tashin hankali: Dan Acaba yayi hadari ya mutu ya bar mata 6 da 'ya'ya 30

- Makomar wasu mata masu takaba shida da yara 30 ta sagale a iska

- Wadannan dai iyalan Mafabi ne, dan achaba mai shekaru 51 da mota ta nike kuma ya bar tarin iyalai

- A halin yanzu dai ana nema musu taimakon jama'a ne don samun ciyar da matan da yaran da ya mutu ya bari

Makomar wasu mata masu takaba shida ya 'ya'ya 30 ta sagale sakamakon mutuwar wani dan achaba wanda suka dogara dashi.

Dan achaban ya rasu ne sakamakon hatsari. Hakan kuwa ya bar mata shida cikin takaba da yara 30 marayu.

Rahoto ya nuna cewa, Hassan Mafabi mai shekaru 51 dan asalin kasar Uganda ne da ya dau bashi ya siya babur don yin achaba. Ba a yi wata da hakan bane yayi hatsari da yayi ajalinshi.

Kamar yadda Ugandans.com ta ruwaito, mamacin ya afkawa wata mota ce mai mugun gudu, lamarin da ya kawo ajali.

KU KARANTA: Hanya daya da namiji zai samu tsawon rayuwa ita ce ya nesanci mace - Tsohon shugaban kasar Kenya

Wani malamin addinin kirista mai suna James William Ssebagalla na cocin Mukono dake Uganda ne ya tabbatar da abun alhinin na mutuwar Mafabi. Ya bayyana cewa iyalinshi ne abun tausayi a wannan lamarin.

Tuko.co.ke sun ruwaito cewa, faston ya fara nemawa iyalan dauki da taimako.

Rayuwar marayu 30 ta sagale sakamakon auren fiye da mace daya da mahaifinsu yayi. Hakazalika rayuwar wasu masu takaba shida ta tsaya cak sakamakon dogaro da suka yi da mijinsu don kula.

A halin yanzu karin tashin hankalin shine wanda zai biya kudin wannan babur din da ya karba a bashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel