Yadda Dasuki ya yi amfani da Sojojin haya daga kasashen wajen murkushe Boko Haram

Yadda Dasuki ya yi amfani da Sojojin haya daga kasashen wajen murkushe Boko Haram

Tsohon shugaban sha’anin mulki a shelkwatar rundunar Sojan sama, Air Vice Marshal Alkali Mohammed Mamu ya bayyana ma wata babbar kotun tarayya a shekarun baya rawar da tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki ya taka wajen murkushe Boko Haram.

Jaridar Desert Herald ta ruwaito Mamu ya bayyana haka ne a ranar 13 ga watan Oktoba na shekarar 2017 yayin daya gurfana a gaban kotu inda yace Dasuki ya dauko sojojin haya daga kasashen waje da suka taimaka wajen yaki da ta’addanci.

KU KARANTA: Malam El-Rufai ne kadai ke da hurumin sakin Sheikh Zakzaky – gwamnatin tarayya

A jawabinsa, Mamu ya shaida ma kotun cewa Dasuki ya dauko sojojin hayan ne da nufin taimaka ma rundunar Sojan sama, inda suka yi basaja tamkar matuka jirgin rundunar Sojan sama, suka dinga sarrafa jiragen yakin rundunar suna ragargazan Boko Haram.

A cewar Mamu wannan ya faru ne tun daga tsakiyar shekarar 2014 zuwa karshen shekarar, a lokacin da rundunar Sojan saman ta gagara tabuka komai, don haka haka Dasuki ya umarce shi ya hada kai da wani mutumi Hima Abubakar daga kamfanin Societe D’Equipments Internationaux Nigeria Limited don dauko sojojin haya da zasu taimaka ma dakarun Najeriya.

“Abubakar ya dauko hayan Sojojin haya matuka jirgin sama guda uku daga Ukraine, wasu sojojin sa kai da ake kira ‘Soldiers of fortune’ da kuma wasu tsofaffin Sojoji da suka bayyana shirinsu na shiga yakin.” Inji shi.

Daga karshe Mamu ya shaida ma kotun cewa daga cikin Sojojin hayan matuka jirgin, akwai wani Kyaftin Chup Vasyl wanda ya mutu yayin da jirginsa ya fadi a lokacin da yake kai ma Boko Haram hari da daddare, inda yace daga bisani gwamnati ta biya iyalansa kudin fansa $100,000.

A wani labarin kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.

Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudin makamai dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel