Babu ‘baraka tsakanina da fadar shugaban kasa – Hajiya Sadiya Umar Farouq

Babu ‘baraka tsakanina da fadar shugaban kasa – Hajiya Sadiya Umar Farouq

Ma’aikatar harkokin agaji, anoba da ci gaban jama’a ta karyata ikirarin cewa fadar Shugaban kasa ta soki ministar ma’aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Misis Rhoda Ishaku Iliya, mataimakiyar daraktan labarai ta ma’aikatar ta bayyana hakan a wani jawabi a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba, a Abuja yayinda take martani ga wasu rahotannin yanar gizo da ke zargin cewa fadar Shugaban kasa ta soki Sadiya.

Ta kara da cewa babu wani lokaci da fadar Shugaban kasa ta soki ministar a kan yawan amfani da iko da daukar ma’aikata aiki fiye da karfin aljihun ma’aikatar.

“Ministar bata taba daukar kowani ma’aikacin agaji ba, domin akwai tsare-tsaren daukar ma’aikata a ma’aikatun gwamnatin tarayya kuma ministar ba za ta iya aiwatar da hakan ba.

“An turo ma’aikatan ma’aikatar ciki harda ma’aikatan ministar ne daga wasu ma’aikatu wanda har yanzu albashinsu na tare da wadannan ma’aikatun.

“Ministar bata taba dakatar da biyan kudin shirin ciyar da dalibai ba. Ya zama dole a ambaci cewa ministar ta amince da biyan kudin shirin har zuwa ranar 31 ga watan Janairu 2020.

“Ma’aikatar na fatan sake jadaddawa jama’a cewa duk wani mataki da minista da mahukuntan ma’aikatar suka dauka daidai yake da tsare-tsare da dokoki.

“Muna rokon masu kawo rahoto da su tabbatar da cewar sun bi tsarin koyarwar aikinsu sannan su dunga tabbatar da labarai kafin su watsa su ga duniya.

“Su sanya ra’ayin jama’a sama a sauran ra’ayoyi wajen aiwatar da ayyukansu,” inji ta.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka yi cushen naira biliyan 264 cikin kasafin kudin 2020 da Buhari ya sa hannu

Ta yi kira ga yan Najeriya da kada su bari wannan kagaggen labari da aka shirya don janye hankalin ministar da gwamnati mai mulki daga magance talauci, da kuma samar arziki ya karkatar da tunaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel