Assha: Yadda jami'in DSS ya harbe wani mutum a kokarin sa na harbe san Kirsimeti

Assha: Yadda jami'in DSS ya harbe wani mutum a kokarin sa na harbe san Kirsimeti

Wani jami'in hukumar 'yan sandan farar hula DSS ya kashe wani mutum mai suna Onyeocha Umuokwu a garin Alor a karamar hukumar Idemili ta Kudu na jihar Anambra.

An gano cewar lamarin ya faru ne a ranar bikin Kirsimeti wato ranar 25 ga watan Disamban 2019.

The Punch ta ruwaito cewa an gano jami'in ya harba harsashi ne don bindige wani shanu da ya tsere daga gidan wani mai hannu da shuni amma harsashin ya fada wa mutumin.

Wata majiya da ta yi tsamannin jami'in na DSS dan sanda ne ya ce, "Dan sanda ne ya harbe Onyeocha Umuokwu a gidan Mista Emeka Eze a ranar 25 ga watan Disamban 2019 a Alor.

"Wani sa da aka daure ya tsinka ingiyar da aka daure ta da shi ya kuma fara gudu. Dan sanda da ke gadi ya saita bindiga don ya harbi san amma harsashin da kubce da kashe Onyeocha Umuokwu. Abin bakin ciki."

DUBA WANNAN: Giwaye 250 aka hango a filin dagar Boko Haram

Ya ce, "An janyo hankalin rundunar 'yan sandan jihar Anambra kan wani labarin mara gaskiya da ke yaduwa a kafafen labarai na cewa dan sanda ya harbe wani Onyeocha Umuokwu a gidan Injiniya Eze a ranar 25/12/2019 a garin Alor, karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

"Akwai yiwuwar wasu marasa kishin kasa da ke son batawa rundunar 'yan sanda suna ne suke yadda labarin da babu kanshin gaskiya a ciknsa.

"Ainihin abin da ya faru shine a ranar 25/12/2019 wani jami'in DSS da har yanzu ba a gano wanene ba a gidan Injiniya Emeka Eze na kauyen Umuokwu ya harba bindiga don tsayar da wani shanu da ya tsere daga gidan amma harsashin da samu wani ma'aikacin gidan Nnaemaka Nnabuenyi da aka fi sani da Onyeocha da ya mutu nan take. Ba a kai rahoton abin wurin 'yan sanda ba.

Mohammed ya kara da cewa, "Bayan afkuwar lamarin, 'yan sanda karkashin jagorancin DPO na Nnobi sun ziyarci wurin amma da Injiniyan da 'yan uwansa duk ba su bayar da wani bayanni mai amfani da zai taimakawa 'yan sanda wurin binciken su ba.

"Sai dai an kai gawar mutumin zuwa asibiti don tabbatar da sanadin mutuwarsa yayin da ake gudanar da bincike kan afkuwar lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel