Gidauniya ta yaye dalibai mahadattan Al- Kur'ani 150 a Ibadan

Gidauniya ta yaye dalibai mahadattan Al- Kur'ani 150 a Ibadan

Gudauniyar Al-Ihsan da aka fi sani da Good People Charity Foundation a Ibadan ta yaye mahadattan Kurani 150 a cikin shekara guda a karkashin shirin ta na haddar Al-Kur'ani mai girma.

Mahaddatan da aka ya ye a taron da aka gudanar da Cibiyar Larabci ta Najeriya, Elekuro, Ibadan sun hada da maza 122 da mata 28 kuma cikinsu 17 marayyu ne.

Shugaban gidauniyar, Sheikh Ahmad Olayiwola ya shawarci wadanda aka ya ye su kasance masu koyi da darussan da suka koya cikin Al-Kur'ani mai girma a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya ce, "Ina kira ga daliban da muka yaye har da na baya su kasance masu tilawar Kur'ani a ko yaushe domin kada haddar da suka yi ta gushe. Su kiyaye sauraron wake-wake da zantuka marasa amfani kuma su yi kokarin koyar da wasu daliban domin cigaban yadda addinin musulunci."

DUBA WANNAN: Giwaye 250 aka hango a filin dagar Boko Haram

Sheikh Olayiwola ya kuma ce gidauniyar ta fara daukan sabbin dalibai.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya masu hannu da shuni su rika tallafawa marasa galihu da masu bukata a garuruwansu.

Sheikh Olayiwola ya kuma ce gidauniyar da aka kafa domin kawo gyara a cikin al'umma ta hanyar bayar da ilimin boko da na islama ta yi nasarar gina masallatai da makarantu 65 ta kuma tallafawa marayu 330 ta fanin ciyarwa da wasu bukatunsu.

Wakilan Good People Charity Foundation biyu da suka taho daga kasar Saudiyya, Sheikh Abdullahi bn Ahmad-Alyahaya da Sheikh Abdul'Azeez bn Muhammad-Atuwajiri sun bayyana gamsuwarsu kan yadda daliban da aka yaye suka karanto Al-Kur'ani tare da ba su kyaututukan kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel