Boko Haram: Rundunar sojin Najeriya ta sake kwato kauyen Fadama, ta samo Qur’anai

Boko Haram: Rundunar sojin Najeriya ta sake kwato kauyen Fadama, ta samo Qur’anai

Rundunar sojin Najeriya tace dakarun Operation Lafiya Dole a karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa a ranar Talata sun yi gagarumar nasara kan yan ta’addan Boko Haram a yankin.

Jagoran labarai na rundunar sojin Najeriya, Aminu Iliyasu, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, a Abuja.

Mista Iliyasu, wanda ya kasance kanal, ya bayyana cewa an samu nasarar ne lokacin da dakarun sojin suka guanar a ayyukan kakkaba kan sauran mayakan Boko Haram da ISWAP daga Madagali ta Waga Lawan, Jaje da Fadama ukka a karamar hukumar Madagali da ke Adamawa.

A cewarsa, an lallasa sauran yan ta’addan ba da wasa ba, inda aka tursasa su tserewa daga wajen.

“Kayayyakin da aka kwato daga yan ta’addan sun hada da kekuna biyu, kwafin Qur’anai da sauran abubuwa da dama. Cikin ikon Allah babu wanda ya mutu daga bangaren hazikan sojin,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Babu wata kalma mai kama da Kirsimeti a littafin Injila – Babban Fasto

Mista Iliyasu ya kuma bayyana cewa dakarun 151 Bn, sashi 1 na Operation Lafiya Dole, sun yi gagarumar nasara kan yan ta’adda a safiyar ranar 25 ga watan Disamba yayin kakkaba da suka gudanar a dajin Sambisa.

Ya kara da cewa an kashe wani dan kunar bakin wake guda wanda ya yi kokarin shiga cikin sansanin dakarun da taimakon wuta a yankin baki daya

A cewarsa, bam din da ke jikinsa ya tashi a hakan sannan aka gano sassan jikinsa a tarwatse.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel